Lafiya Uwar Jiki
Da yake bayyana yadda lamarin ya afku, Dakta Ajayi, aboki ga marigayin, ya ce: "Victoria Popravko ta gayyaci Gbolade Ejemai gidanta a ranar Jama'a, 8 fa watan Agusta, 2019, domin su tattauna wasu maganganu. "Babu wanda ya zargi
Najeriya na daya daga cikin yanki na karshe a duniya da cutar shan inna ta samu wurin zama, sai dai wani sabon bincike ya tabbatar da cewa sauran kiris kasar ta tsarkaka da wannan cuta da zamto alakakai tsawon shekaru aru-aru.
Mun samu cewa an samu nasarar gano maganin cutar Ebola da ta ki ci ta ki cinyewa a wasu kasashen yankin Afirka yayin da aka sallami wasu mutane biyu daga wata cibiyar gwaji dake gabashin jamhuriyyar Dimokuradiyyar Kongo.
Jami'an 'yan sanda sun samu gawar Ilona a rataye a gidanta da ke unguwar Neath a yankin Port Talbot a kudancin Wales bayan makwabtanta sun kira su. Makwabtan Ilona sun kira jami'an 'yan sandan ne da safiyar ranar 6 ga watan Agusta
Kwararrun lafiya na kasar Habasha sun tabbatar da cewa, Mista Odemu ya yi ido biyu da ajali bayan da cutar kajamau wadda ta shahara da karya duk wata garkuwar jiki ta yi masa rikon kazar kuku da a dole sai da ta kai shi ga faduwa.
Tsawon shekaru aru-aru 'baure wani nau'in dangin kayan marmari ne da ya shahara a duniya ta fuskar dandano da kuma amfani ga lafiya. Wani bincike da jaridar Guardian ta wallafa ya bayyana muhimmancin baure wajen magance cututtuka.
Kankana ta kasance daya daga cikin 'ya'yan itatuwa mafi shahara a doron kasa kuma mutane da dama su kan yi santi kwarai yayin kwankwadar ruwanta musamman wadanda kwayoyin halittun su masu bambance dandano ke aiki kwarai.
Idan aka ce Hepatitis, toh ana nufin ciwon Hanta kenan a Hausance. Hepatitis kasu iri daban-daban har guda biyar, inda suka hada da; Hepatitis A, Hepatitis B, Hepatitis C, Hepatitis D, Hepatitis E.
A yau ne ranar ciwon hanta ta duniya wato World Hepatitis Day. Allurar riga kafin ciwon hanta wasu allurori ne guda uku zuwa hudu da ake yi na tsawon watanni 6. Ba'a kamuwa da ciwon hanta matukar an yiwa mutum alluran riga kafi.
Lafiya Uwar Jiki
Samu kari