Rukunan mutane 13 da ya kamata a yiwa allurar riga kafin ciwon hanta

Rukunan mutane 13 da ya kamata a yiwa allurar riga kafin ciwon hanta

A yau ne ranar ciwon hanta ta duniya wato World Hepatitis Day.

Allurar riga kafin ciwon hanta wasu allurori ne guda uku zuwa hudu da ake yi na tsawon watanni shida. Ba'a kamuwa da ciwon hanta matukar an yiwa mutum alluran riga kafin cutar.

Rukanan mutanen 13 da aka shawarta suyi allurar rigakafin ciwon hanta sun hadar da:

1. Jarirai sabuwar haihuwa

2. Kananan yara da kuma masu tashen balagar fari wadanda ba a yiwa rigakafi ba bayan haihuwar su.

3. Wadanda suke aiki ko kuma rayuwa a alkaryoyin da babu ci gaba.

4. Wadanda ke zama ko kuma rayuwa cikin masu cutar Hepatitis B

5. Ma'aikatan lafiya da kuma ma'aikatan bayar da agajin gaggawa da kuma wadanda ke alaka da jini.

6. Wadanda suka kamu da kowace irin cuta ta hanyar saduwa, da suka hadar da cuta mai karya garkuwar jiki wato HIV.

7. Masu yawaita saduwa da mutane daba-daban musamman karuwai.

8. Masu abokin saduwa mai dauke a cutar musamman miji ko mata.

9. Masu yiwa kawunan su alluran kwayoyi na maye.

KARANTA KUMA: Fatan alheri kan jihar Imo ya sa Buhari ya yiwa Nwajubu nadin minista - Uzodinma

10. Mutane masu matsananciyar cuta hanta.

11. Masu matsananciyar cutar koda.

12. Matafiya masu niyyar kai ziyara yankunan da cutar hanta tayi kamari.

13. Maza masu neman 'yan uwan su maza.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng