Mutane dubu 90 sun kamu da cutar kyanda a nahiyyar Turai - UN
Hukumar lafiya ta Duniya WHO, ta bayyana cewa, cutar kyanda ta sake bulla a nahiyyar Turai, inda alkalumman da fitar a baya-bayan nan ke nuni da cewa kimanin mutane dubu 90 ne suka kamu da cutar a tsakanin watan Janairu zuwa Yunin shekarar da muke ciki.
A wani rahoto da majalisar dinkin duniya reshen kula da lafiya ya fitar a ranar Alhamis, ya danganta sake bullar cutar kyanda da nokewar al'umma wajen karbar maganin rigakafin cutar.
Majalisar ta ce a tsakanin watan Janairu zuwa watan Yunin shekarar da muke ciki, adadin wadanda suka kamu da cutar kyanda a duniya baki daya ya ninku sau biyu idan an kwatanta da da shekarar bara ta 2018.
A cikin rahoton dai da muka kalato daga jaridar RFI Hausa, majalisar dinkin duniya ta ce kasar Ukraine ce ke kan gaba ta fuskar adadin wadanda suka kamu da cuta, inda mutane sama da dubu 84 suka harbu yayin da kuma kasar Kazakhstan, Georgia suka biyo baya.
Kasar Jamus ta kasance a mataki na hudu inda akalla mutane 400 suka kamu da cutar ta kyanda kuma mafi akasari suka kasance yara.
KARANTA KUMA: Kashi 3% cikin ma'aikatan mu sun dabi'antu da rashawa - EFCC
Dakta Guenter Pfaff, shugaban hukumar lafiya ta duniya reshen yaki da cutar kyanda, shi ne ya bayar da wannan rahoto, inda ya ce ya zuwa yanzu, kasashen Albania, Jamhuriyar Czech, Girka da kuma Birtaniya, sun sauka daga matakin da suke kai a baya, na samun nasarar fatattakar cutar kyanda daga cikin al’ummominsu.
A wata kididdiga da majalisar dinkin duniya ta fitar a shekarar 2017, ta ce akalla mutane dubu 110 ne suka rasa rayukansu a sanadiyar kamuwa da cutar kyanda, inda ta ce mafi akasari sun kasance yara 'yan kasa da shekaru biyar a duniya.
Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng