Kaico: 'Yan KAROTA sun haddasa mummunan hatsari a Kano, jami'in hukumar KSSC ya mutu

Kaico: 'Yan KAROTA sun haddasa mummunan hatsari a Kano, jami'in hukumar KSSC ya mutu

Wani mai bayar da horo a bangaren motsa jiki a hukumar wasanni ta jihar Kano (KSSC), Baba Yusuf, ya rasa ransa ranar Asabar a wani hatsarin mota da ya ritsa da shi a kan titin 'Club Road' a cikin kwaryar birnin Kano.

A cewar wani shaidar gani da ido, hatsarin ya ritsa da marigayin ne yayin da yake tuka babur dinsa domin zuwa wurin aikinsa bayan ya baro gidansa dake unguwar 'Birged' a karkashin karamar hukumar Nasarawa.

Shaidar ya bayyana cewa wata motar fasinja ce kirar 'Golf' ta ture Baba Yusuf tare da taka shi a yayinda suke tsere da jami'an hukumar kula da dokokin tuki a birnin Kano (KAROTA).

"Jami'an KAROTA ne suka biyo motar, sun yi kokarin tsayar da direban ta kowacce hanya domin sun yi kokarin kwace motar ta hanyar kokarin karbe sitiyarin motar bayan sun cimma sa duk da kasancewar bai tsaya ba. Yayin kokawar kwace tukin motar daga hannun direban ne sai ta kwace, ta buge Baba Yusuf yayin da yake tuka babur dinsa, kuma nan take ya mutu.

"Sai da jama'ar dake gefen hanya suka taru sannan aka iya zaro gawar Baba Yusuf daga karkashin motar bayan ta taka shi tare da babur dinsa," a cewar shaidar.

Kazalika, shaidar ya bayyana cewa lamarin ya fusata jama'a inda suka yi wa jami'in KAROTA rubdugu da 'duka' kafin wasu jami'an 'yan sanda da suka zo wuce wa su kwace shi da kyar.

DUBA WANNAN: 'Yan Boko Haram sun kai wa tawagar sojoji hari, sun debi kudi da muhimman kayayyaki

Wannan ba shine karo na farko da jami'an KAROTA suka haddasa hatsari da ya yi sanadiyar rasa rai ba a birnin Kano.

Kakakin hukumar KSSC, Sabo Abbati, ya tabbatar da faruwar lamarin ga wakilin jaridar Solacebace.com a birnin Kano.

Ya ce sun yi matukar kadu wa da samun labarin mutuwar Baba Yusuf, mutumin da ya ce ya kasance ma'aikaci a hukumar KSSC na tsawon fiye da shekaru 20.

Kazalika, kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Kano, DSP Abdullahi Kiyawa, ya tabbatar da kama jami'in KAROTA da ya haddasa hatsarin.

Kaico: 'Yan KAROTA sun haddasa mummunan hatsari a Kano, jami'in hukumar KSSC ya mutu
Baburin marigayi Baba Yusuf a wurin da mota ta buge shi
Asali: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng