Kiwon Lafiya: Amfani 15 na 'baure ga lafiyar dan Adam
Tsawon shekaru aru-aru, 'baure wani nau'i ne na dangin kayan marmari da ya shahara a duniya ta fuskar dandano da kuma amfani ga lafiya. Wani sabon bincike da jaridar Guardian ta wallafa ya bayyana muhimmancin baure wajen magance cututtuka da dama kama daga ciwon suga zuwa cututtukan fata.
'Baure ya kunshi sunadarai da dama masu gina jiki da suka hadar da fiber, antioxidants, vitamin A, vitamin C, vitamin K, B vitamin, potassium, magnesium, zinc, copper, manganese da kuma iron.
Wani bincike da aka gudanar a shekarar 2016 ya tabbatar da cewa, sunadarin ficusin da dan itaciyar baure ya kunsa na taka rawar gani wajen magance radadin ciwon suga.
Ga wasu kadan daga cikin tasiran da baure ke yi wajen magance cututtuka da kuma bunkasa lafiyar jikin dan Adam:
1. Magance kwarnafi da tashin zuciya.
2. Hawan jini.
3. Bunkasa lafiyar zuciya da jini.
4. Ciwon daji wato cutar Kansa.
5. Rage nauyin jiki.
6. Inganta lafiyar mazakuta da kuma ni'imar ma'aurata.
7. Magance ciwon basir mai tsuro.
8. Cutar farfadiya.
9. Tace mafitsara.
10. Tasiri wajen inganta lafiyar fata.
KARANTA KUMA: Ya kamata gwamnati ta yi wa Zakzaky adalci - Bala Lau
11. Zazzabi.
12. Ciwon Kunne.
13. Cututtukan fata (Karzuwa, makero, maruru, kirci, kyazbi).
14. Bunkasa lafiyar hanta.
15. Cutar asma da dangin cututtukan da suka shafi hunhu.
Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng