Cutar kanjamau ta kashe dan Najeriya Odemu Efe a kasar Habasha

Cutar kanjamau ta kashe dan Najeriya Odemu Efe a kasar Habasha

A ranar Talatar da ta gabata, hukumar kula da harkokin waje da 'yan Najeriya mazauna ketare NIDCOM, ta ce wani dan Najeriya Mista Odemu Efe da ke cin sarka ta tsawon shekaru biyar a wani gidan yari na kasar Habasha, ya riga mu gidan gaskiya a sanadiyar cutar kanjamau mai karya garkuwar jiki.

Shugaban cibiyar sadarwa na hukumar, Mista Abdurrahman Balogun, shi ne ya bayar da shaidar hakan cikin wata sanarwa a yayin ganawa da manema labarai cikin garin Abuja. Ya ce Mista Odemu ya bar duniya bayan shekara daya kacal cikin biyar da ya kamata ya shafe a gidan kaso.

Sabanin rade-radin da ke yaduwa na cewar Mista Odemu ya mutu ne a sanadiyar azabtarwa gami da rashin samun wadattacen abinci yayin da yake daure, hukumar NIDCOM ta ce ajali ya katse masa hanzari bayan cutar SIDA ta kwashi rabonta inda ya galabaita kuma a karshe ya ce ga garinku nan.

Kwararrun lafiya na kasar Habasha sun tabbatar da cewa, Mista Odemu ya yi ido biyu da ajali bayan da cutar kajamau wadda ta shahara da karya duk wata garkuwar jiki ta yi masa rikon kazar kuku da a dole sai da ta kai shi ga faduwa.

Ofishin jakadancin Najeriya dake kasar Habasha, yayi bayar da shaida ya ce an garzaya da marigayi Odemu har zuwa wasu cibiyoyin lafiya daban-daban a birnin Addis Ababa gabanin cikawar sa.

KARANTA KUMA: Gwamnatin Kaduna ta nemi haramtawa Zakzaky izinin tafiya kasar Indiya

Mista Balogun ya yi watsi da ikirarin cewa ana nuna wa 'yan Najeriya banbanci da kuma wariyar launin fata musamman ta fuskar kula da jin dadin su a gidajen kaso na kasar Habasha.

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, laifin fataucin miyagun kwayoyin ya sanya kotun kasar Habasha ta yankewa marigayi Odemu hukuncin dauri na tsawon shekaru biyar a gidan dan Kande.

Shugaban hukumar NIDCOM ta Najeriya, Abike Dabire Erewa, ta jajantawa 'yan uwan marigayi Odemu tare da yin addu'a ta neman Mai Duka ya jikansa.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng