Mutane 2 sun warke daga cutar Ebola a Kongo

Mutane 2 sun warke daga cutar Ebola a Kongo

Mun samu cewa an samu nasarar gano maganin cutar Ebola da ta ki ci ta ki cinyewa a wasu kasashen yankin Afirka yayin da aka sallami wasu mutane biyu daga wata cibiyar gwaji dake gabashin jamhuriyyar Dimokuradiyyar Kongo.

Jaridar BBC Hausa ta ruwaito cewa, mutanen biyu da aka sallama suna cikin mutanen da cutar Ebola ya yiwa rikon kazar kuku a garin Goma, wato garin da ya fi fama da annobar inda akalla mutane 1800 suka mutu.

Da yake dai gwaji na tafiya hannu da hannu da yiwuwar samun nasara ko kuma kishiyar hakan, wasu mutane biyu da aka yi gwajin a kansu sun rasa rayukansu sanadiyar cutar ta Ebola.

Jagoran kungiyar kwararrun likitoci masana kimiyya da suka gudanar da gwajin maganin cutar Ebola, Dakta Sabue Mulangu, ya ce suna kyautata zaton ana gab da samu rigakafin cutar bayan samun nasarar da aka yi wajen gwajin maganin ta har nau'ika biyu.

Da wannan ne Dakta Mulangu ya ce yana ganin zuwa gaba kadan kaso 60 cikin mutum 681 da suka kamu da cutar za su tsira wajen samun waraka.

An samu nau'ikan magungunan biyu REGN-EB3 da kuma mAb114 daga kwayoyin yaki da cutar da aka samu a jikin wadanda suka tsira daga ita kamar yadda masu binciken suka bayyana.

KARANTA KUMA: Yaki da ta'addanci: Buratai ya yabi sadaukarwar dakarun sojin Najeriya

Sun ce idan aka gaggauta yin magunguna cikin kankanin lokaci, kaso 90 cikin 100 ne na masu dauke da cutar za su samu waraka.

A yayin da hukumar lafiya ta duniya, WHO (World Health Organisation) ta jagoranci gwajin magungunan, ta kuma bayar da sahalewarta a kan fara amfani da magungunan ga dukkanin masu fama da cutar ta Ebola ko in suka a doron kasa.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng