Najeriya na gab da tsarkaka daga cutar shan inna
Najeriya na daya daga cikin yanki na karshe a duniya da cutar shan inna ta samu wurin zama, sai dai wani sabon bincike ya tabbatar da cewa sauran kiris kasar ta tsarkaka daga wannan cuta da zamto alakakai tsawon shekaru aru-aru.
Ana sa ran a ranar 21 ga watan Agusta za a kaddamar da tsarkin Najeriya daga cutar shan inna muddin ba a sake samun wadanda suka kamu da cutar ba kamar yadda kafar watsa labarai ta BBC ta bayyana.
Sai dai daya daga cikin manema labarai na BBC, Ajoke Ulohotse, ta shilla jihar Kano da ke Arewacin Najeriya domin bankado yadda lamarin ke gab da kasancewa.
Mahukunta a jihar Kano sun ce, an samu tsarki na kaso 99 cikin 100 daga cutar shan inna inda suka bankado tarihi kan yadda cutar da rika yi wa yara diban karen mahaukaciya musamman a karamar hukumar Fagge a lokutan baya.
A shekarar 2011, hukumar kula da kiwon lafiya a matakin farko ta Najeriya ta ce, alkalumma na baya-bayan nan sun nuna cewar, yawan wadanda suke kamuwa da cutar shan inna a kasar ya karu.
KARANTA KUMA: Yaki da ta'addanci: Buratai ya yabi sadaukarwar dakarun sojin Najeriya
A wani rahoton mai nasaba da wannan da jaridar Legit.ng ta ruwaito, hukumar lafiya ta Duniya, WHO, ta gano maganin cutar Ebola inda a halin yanzu tuni mutane biyu suka samu waraka a jamhuriyyar Dimokuradiyyar Kongo.
Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng