Jerin illoli 7 da ke tattare da shan ruwan sanyi ciki harda sa mutum tsufa da wuri

Jerin illoli 7 da ke tattare da shan ruwan sanyi ciki harda sa mutum tsufa da wuri

Wani kwararren likitan yara mai suna Ovo Ogbinaka yayi sharhi aka illar da ke tattare da yawan shan ruwan sanyi a jikin dan adam.

A wata hira da yayi da kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a jihar Edo, likitan ya bayyana cewa ya gano hakan ne a wani bincike da ya gudanar akan shan ruwan sanyi da kuma kalubalen da ke tattare da shi.

Ya ce sakamakon binciken ya nuna cewa yawan shan ruwan sanyi na sa mutum ya tsufa da wuri sannan kamuwa da cututtukan dake kama hakarkari da zuciya.

Ya kara da cewar ba a iya gane illar shan ruwan sanyi sai mutum ya fara tsufa.

KU KARANTA KUMA: Innalillahi wa’inna illaihi raji’un: Barayi sun kashe wani babban dan kasuwa, sun tsere da N590,000

A cewarsa idan har ya kama a sha ruwa mai sanyi kamata ya yi a rage sanyin ruwan kafin a sha domin rashin yin haka ne ke cutar da kiwon lafiyar mutum.

Dalla-dalla; ga jerin illolin da ke tattare da shan ruwan sanyin:

1. Shan ruwan sanyi na kawo mura,tari da toshewar murya.

2. Ruwan sanyi na sa mutum tsufa da wuri

3. Ya hana narkar da abinci a cikin mutum.

4. Shan ruwan sanyi na haddasa taruwan kitse a kodar mutum.

5. Yana daskarar da jijiyoyin jiki wanda hakan ke hana jini gudana.

6. Shan ruwan sanyi na sa kirji ya yi ta ciwo.

7. Yana kuma lalata hanji da hakan ke sa a kamu da ciwon daji.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel