Wata baturiya da mahaifinta sun kashe likitan Najeriya ta hanyar caccaka masa wuka

Wata baturiya da mahaifinta sun kashe likitan Najeriya ta hanyar caccaka masa wuka

Wani matashi dan Najeriya da ke karatun likitanci a kasar Ukraine ya mutu sakamakon caccaka masa wuka da wata mata ta yi.

Matashin likitan mai suna Gbolade Ibukun Ejemai ya mutu ne bayan wata mata mai suna Victoria Popravko ta caccaka masa wuka kafin daga bisani mahaifinta ya saka guduma ya buge shi a ka.

Da yake bayyana yadda lamarin ya afku, Dakta Ajayi, aboki ga marigayin, ya ce: "Victoria Popravko ta gayyaci Gbolade Ejemai gidanta a ranar Jama'a, 8 fa watan Agusta, 2019, domin su tattauna wasu maganganu.

" Babu wanda ya zargi wani abu saboda wannan ba shine karo na farko da ta gayyace shi gidanta ba, musamman kasancewarsu masoya.

"Babu wanda ya san menene ya shiga tsakaninsu har ta kai ga Victoria ta caccaka wa Gbolade wuka a ciki bayan sun tafka mahawara, lamarin da ya kai ga ta illata wasu kayan cikinsa.

DUBA WANNAN: Kungiyar IPOB ta fadi dalilinta na cin mutuncin Ekweremadu a kasar Jamus

"An garzaya da shi asibiti domin a ceto rayuwarsa, sai da muka shafe awanni 24 muna jira kafin ya samu daga bisani ya iya bude idonsa ya gane inda ya ke da kuma su waye ke tare da shi.

"Bayan ya farka ne ya sanar da mu a kan yadda mahaifin Victoria ya saka guduma ya buge shi a ka bayan ya fahimci cewa bai mutu ba bayan wukar da diyarsa ta caccaka masa."

A cewar Ajayi, lafiyar Gbolade ta kara sukurkuce wa ranar Litinin kafin daga bisani ya mutu ranar Talata.

Ajayi ya bayyana cewa zasu cigaba da magana a kan kisan gillar da aka yi wa Gbolade har sai an dauki mataki a kan Victoria da mahaifinta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng