Wata budurwa ta rataye kan ta saboda ta yi cikin shege

Wata budurwa ta rataye kan ta saboda ta yi cikin shege

Jami'an 'yan sanda sun samu gawar wata matashiya, Ilona Grant, mai shekaru 23, wacce ta rataye kan ta a gidanta bayan ta gano cewa tana dauke da juna biyu.

Ilona ta kashe kan ta be kwana daya bayan ta sanar da saurayinta cewa tana dauke da juna biyu, kuma tana son zubar da shi.

Jami'an 'yan sanda sun samu gawar Ilona a rataye a gidanta da ke unguwar Neath a yankin Port Talbot a kudancin Wales bayan makwabtanta sun kira su.

Makwabtan Ilona sun kira jami'an 'yan sandan ne da safiyar ranar 6 ga watan Agusta bayan sun ji tana daga murya yayin musayar yawu da sauarayinta a ranar 5 ga watan Agusta.

DUBA WANNAN: Da duminsa: Kotu ta bawa EFCC izinin tsare tsohon shugaban INEC

Kwana daya kafin ta kashe kan ta, Ilona ta ziyarci kwararren da ke duba ta, saboda tana da matsala a kwakwalwar ta, tare da sanar da shi cewa dauke da juna biyun wata guda, kuma tana son zubar da shi. Lamarin da yasa mai duba lafiyar ta ya kira saurayint tare da sanar da shi halin da ake ciki.

Ana zargin cewa Ilona ta fasa kwalbar giya a jikin bango tare da yi wa kan ta rauni kafin daga bisani ta rataye kan ta, kamar yadda jami'an 'yan sanda suka sanar bayan sun isa gidan da ta rataye kan ta.

Mai kula da matsalar Ilona, Colin Philips, ya ce matashiyar ta kashe kan ta ne saboda rashin isashiyar kulawa da goyon bayan da take bukata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng