NTCA ta roki Buhari ya kara kudin haraji a kan ganyen taba sigari
NTCA (Nigeria Tobacco Control Alliance), wata kungiya mai rajin yaki da zukar hayakin ganyen taba sigari barkatai, ta roki gwamnatin tarayya ta kara kudin haraji a kan dukkan abubuwan da ake sarrafa wa daga ganyen tabar sigari da ake shigo wa da su cikin Najeriya.
Kungiyar ta bayar da wannan shwara ne ranar Alhamis a Abuja yayin wani taro da ta shirya tare da hadin gwuiwar sauran kungiyoyi masu neman a takaita amfani da ganyen tabar sigari a fadin kasa.
A wurin taron da ya samu halartar masu ruwa da tsaki da jami'an gwamnati, NCTA ta ce kara kudin haraji a kan ganyen tabar sigari zai taka muhimmiyar rawa wajen daukan matakan rage yadda ake amfani da karan tabar sigari barkatai a lunguna da sako na kauyuka da biranen da ke Najeriya.
DUBA WANNAN: Tsohon gwamnan APC ya saci tiriliyan daya a cikin shekaru 8 - Gwamnan PDP
NCTA ta ce kara yawan kudin harajin zai kawo raguwar annobar amfani da karan taba sigari da jama'a ke yi barkatai.
Kungiyar ta bayyana cewa Najeriya na samun kudin shiga fiye da biliyan N10 duk shekara daga harajin ganyen tabar sigari tare da bayyana cewa gwamnati ba ta amfani da koda kaso 10% na kudin domin kawo tsari ko kirkirar dokokin da zasu takaita amfani da ganyen a cikin kasa.
Kazalika, kungiyar ta yi kira ga gwamnatin tarayya da take amfani da kudaden harajin ganyen tabar sigari wajen inganta bangaren kula da lafiyar jama'a.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng