Amfanin ganyen dalbejiya guda 16 a jikin dan adam
- Itacen dogon yaro ko kuma dalbejiya ya kasance mai matukar amfani ko a la’adar bahaushe
- Yana yin magunguna daban-daban na cutukan da ke addabar jikin dan Adam
- Ganyen na tsarin iyali, maganin dafi, maganin kwari,hana kamuwa da cutukan jima’i da sauransu
Itacen dogon yaro ko kuma dalbejiya ya kasance ice mai matukar amfani ko a al’adar bahaushe. Ana kiran itacen da ‘Neem tree’ a turance. Tana da daci amma tana da matukar amfani a jikin dan Adam.
Ga wasu amfanin dalbejiya a jikin mutum:
1. Ganyen dalbejiya na kare mutum daga kamuwa da cutar bugawar zuciya, musamman idan aka dafa ganyen ana shan ruwan kamar shayi.
2. Yana taimakawa wajen tacewa da tsaftace jinin jikin mutum.
3. Ganyen na maganin cutar zazzabin cizon sauro da typhoid.
4. Yana maganin cutar ciwon ciki, musamman idan mutum ya murde saboda wani abinci da aka ci.
5. Ganyen dalbejiya da man shi na gyara fatar jikin mutum.
6. Ganyen na maganain saiko, amosanin kai da kuma sa tsawon gashin kai.
7. Ana iya amfani da man dalbejiya a matsayin dabarar bada tazarar iyali.
8. Ganyen na kawar da cutar daji, musamman na nono da ‘ya’yan maraina.
KU KARANTA: Tirkashi: Wata mata ta gano yadda aminiyarta da suka shekara 25 suna tare ta aure mata miji
9. Ganyen na maganin cutar gyambon ciki da rauni a jiki.
10. Yana rage kiba a jiki musamman ga masu fama da ita.
11. Yana warkar da ciwon gabobi da ciwon kai.
12. Yana kare mutum daga kamuwa da cutukan da ake samu ta hanyar yin jima’ai.
13. Yana warkar da cutar kuturta.
14. Yana maganin ciwon ido.
15. Yana maganin guba da ake samu daga jikin dabba kamar cizon cinnaka, maciji da sauransu.
16. Ganyen na maganin kwari musamman wadanda ke lalata amfanin gona.
Asali: Legit.ng