Labaran Duniya
Duniya da fadi yayin da wani matashi mai suna Sohib Ahmad ya siya wa budurwarsa makeken fili a duniyar wata mai girman eka daya don burge ta a Pakistan.
Rayukan mutane da dama sun salwanta bayan gobara ta tashi a wata ma'ajiyar man fetur da aka yi fasa ƙwaurinsa daga Najeriya zuwa Jamhuriyar Benin.
An samu asarar rayukan aƙalla mutum takwas bayan wani jirgin sama na yaƙi na ƙasar Kenya wanda yake ɗauke da sojoji ya yi hatsari. An fara gudanar da bincike.
Ƙasar haɗaɗdiyar daular Larabawa (UAE), ta musanta cewa ta cire haramcin ba matafiya ƴan Najeriya takardar biza domin shiga ƙasar wanda ta ƙaƙaba musu.
Kamfanin jirgi ya kori wani mutumi, matarsa da diyarsu daga cikin jirgi bayan sauran fasinjojin jirgin sun yi korafin cewa suna wani irin wari mara dadin ji.
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna alhininsa bisa ibtila'in ambaliyar ruwan da ya afkawa ƙasar Libya, wacce ta yi sanadin rasuwar sama da mutane 6,000.
Wata mata ƴar ƙasar Kenya wacce ke rayuwa a kusa da rafin Baringo ta bayyana yadda kada ta raba ta da ƙafarta guda ɗaya. Ta ce rayuwa ta koma mai wuya a gareta.
A wani salo da ba a saba gani ba, kasar Faransa na rokon Morocco da ta yi hakuri ta karbi tallafin Yuro miliyan biyar da ta yi niyyar ba ta bayan girgizar kasa.
Wata mummunar ambaliyar ruwa da ta faru a ƙasar Libya ta yi sanadiyyar ɓacewar mutane aƙalla 10,000 tare da halaka wasu da dama. Lamarin ya faru ne a birnin Derna.
Labaran Duniya
Samu kari