Abin Duniya Ya Jawo Rigima Tsakanin Mashahurin ‘Dan Kasuwan Najeriya da Yaransa

Abin Duniya Ya Jawo Rigima Tsakanin Mashahurin ‘Dan Kasuwan Najeriya da Yaransa

  • Gabriele Volpi ya na kotu da ‘ya ‘yansa saboda rigimar mallakar kadarorin kamfanonin da suka kafa
  • Babu jituwa tsakanin ‘dan kasuwan da yaransa tun da aurensa ya mutu da mahaifiyarsu a shekarar 2017
  • An yi kokarin ayi wa gidan sulhu amma abin ya gagara, Attajirin yana neman ganin bayan magadansa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Shekaru shida da suka wuce, rigima ake ta yi tsakanin Gabriele Volpi da yaronsa Matteo a kan dukiya, sabanin ya jawowa dangin shiga kotu.

Premium Times ta kadaita da wani rahoto da ya ce attajirin Najeriyan ‘dan asalin Italiyan yana rigima da babban yaronsa, har abin ya girgiza alkalai.

Rigimar da ta shiga kotun kasashen Najeriya, Bahamasa, Birtaniya da Malta ta yi kamari, dangatakar jinin da ke tsakanin mutanen biyu tayi muni.

Gabriele Volpi
Gabriele Volpi yana rigima da iyalinsa Hoto: www.armadanews.com
Asali: UGC

Wanene Gabriele Volpi?

Kara karanta wannan

Yadda Marigayi Albani Ya Hango Janye Tallafin Man Fetur Shekaru 9 da Suka Wuce

Gabriele Volpi mai shekara 80 a Duniya ya zo Najeriya ne a 1976, kamfaninsa na Noli International Shipping Services Limited ya yi suna tun a 1978.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Attajirin ne ya hada-kai da kamfanin AGIP, ya kafa kamfanin NICOTES, daga baya su ka hadu da Atiku Abubakar a shekarar 1995, su ka kafa INTELS.

A duk kasuwancin da yake yi, Volpi yana cusa yaronsa maza biyu - Matteo da Simone, 2016 abubuwa su ka cabe da ya yi rikici da matarsa, Rosaria.

Auren Volpi ya mutu

Matteo mai shekara 54 ya fadawa kotu cewa mahaifiyarsu watau Nee Rota ta rabu da mahaifinsu a 2017 a sakamakon gano cewa yana neman wata mata.

A dalilin mutuwar auren na su, attajirin ya mallakawa tsohuwar mai dakinsa $100m, kotu ta ce daga ciki Nee Rota ta ba kowane daga cikin ‘ya ‘yanta $20m.

Kara karanta wannan

“A Wannan Marran”: Peter Obi Ya Yi Martani Ga Ma’aikaciyar Otel Da Ta Mayar Da Miliyan 55 Da Ta Tsinta

Yayin da ‘dan kasuwan yake rigima da uwar ‘ya ‘yansa, babban yaronsa watau Matteo shi kuma ya dage wajen karbe kamfanin da kadarorin mahaifinsa.

Matteo da tsohon mai shekara 80 ne Darektocin kamfanin Orlean Invest Holding S.A da aka bude a 1984, kuma yana cikin Darektocin kamfanin nan na Intels.

Matteo ya maka uban shi a kotu

Ba tare da ya sani ba, tsohon ya lallaba ya cire hannun yaron daga kamfanin, abin da ya jawo rikici.

Rahoton ya ce ‘dan kasuwan ya yi haka ne saboda ya hana iyalinsa hakki a cikin kadarorinsa da sun kai $1.2bn. An yi yunkurin yin sulhu, abin ya gagara.

Yanzu haka ana shari’a a kasashen Bahamasa da Malta, kuma an maka Gabriele a wani kotun Ingila, Matteo yana zargin mahaifinsa da kin biyansa bashi.

Matsin lambar tattalin arzikin Najeriya

Masu kuka game da matsin lambar tattalin arziki su dakata, cin kwa-kwa bai kare ba tukuna, a makon nan aka rahoto Bismarck Rewane yana nuna hakan.

Bismarck Rewane ya ce sai an kai shekara mai zuwa kafin abubuwa su daidaita, farashin kudin kasashen waje ya tashi, sannan an cire tallafin man fetur.

Asali: Legit.ng

Online view pixel