Tsohon Shugaban Ƙasar Ivory Coast, Konan Bedie, Ya Rasu Yana da Shekaru 89

Tsohon Shugaban Ƙasar Ivory Coast, Konan Bedie, Ya Rasu Yana da Shekaru 89

  • Tsohon shugaban ƙasar Ivory Coast, Henri Konan Bedie, ya kwanta dama yana da shekaru 89 a duniya
  • Ɗaya daga cikin 'yan uwansa na kusa ne ya tabbatar da rasuwar ranar Talata, 1 ga watan Agusta amma bai yi cikakken bayani ba
  • Marigayin Konan Bedie ya shafe tsawon lokaci ana damawa da shi a fagen siyasar ƙasar kuma ya kafa tarihin da za a riƙa tunawa da shi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Tsohon shugaban ƙasar Ivory Coast, Henri Konan Bedie, wanda ya mamaye siyasar ƙasar da ke yammacin nahiyar Afirka na tsawon lokaci, ya riga mu gidan gaskiya.

Wani ɗan uwansa na kusa-kusa ya bayyana cewa tsohon shugaban ƙasar ya mutu yana da shekaru 89 a duniya ranar Talata, 1 ga watan Agusta, 2023.

Marigayi tsohon shugaban ƙasar Ivory Coast, Henri Konan Bedie.
Tsohon Shugaban Ƙasar Ivory Coast, Konan Bedie, Ya Rasu Yana da Shekaru 89 Hoto: pmnews
Asali: UGC

Har yanzu ba bu cikakken bayani daga iyalansa ko makusanta kan musabbabin da ya yi ajalin tsohon shugaban ƙasar, kamar yadda jaridar Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Sunayen Ministoci: Jerin Iyayen Gida Masu Tasowa a Siyasance Da Ka Iya Zama Ministocin Tinubu

Yayin da aka tuntuɓi mai magana da yawunsa, ba a same shi ba ballantana a nemi ƙarin bayani kan rasuwar mai gidansa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Taƙaitaccen tarihin siyasar Konan Bedie a ƙasar Ivory Coast

Marigayi Bedie ya riƙe kujerar shugaban kasar Ivory Coast tun daga shekarar 1993 har zuwa lokacin da aka fatattake shi a shekarar 1999.

Lokacin yana ɗan shekara 86 a duniya, Konan Bedie ya sake neman zama shugaban ƙasa amma ya sha kaye a hannun babban abokin adawarsa na siyasa, shugaba Alassane Ouattara a zaɓen 2020.

An dade ana tunawa da shi bayan ya bar mulki, amma a wasu sassan ana zaginsa saboda rawar da ya taka wajen haɓaka batun "Ivoirite", ko kuma a ce asalin Ivory Coast.

Rahoton jaridar Vanguard ya nuna cewa wannan batu na 'yan asalin ƙasa ya jefa ruɗani da tashin hankali tsakanin waɗanda suke ganin haifaffun kudanci da gabashin Ivory Coast ne.

Kara karanta wannan

Bayan Taro a Aso Villa, NLC Ta Yi Magana Kan Janye Zanga-Zanga da Shiga Yajin Aikin da Ta Shirya a Najeriya

Bugu ƙari, wannan batu ya haddasa ruɗania tsakanin ma'aikata 'yan kasashen maƙota waɗanda suka samu wurin zama a arewacin ƙasar.

Hawaye Sun Kwaranya Bayan Yariman Babbar Masarauta a Arewacin Najeriya Ya Kwanta Dama

A wani rahoton kuma an shiga jimamin rashin mai girma Yariman Gombe, Alhaji Abdulkadir Abubakar Umar, wanda ya koma ga mahaliccinsa.

Marigayi Alhaji Abdulkadir Abubakar Umar, ya yi bankwana da duniya ne a ranar Talata, 1 ga watan Yulin 2023 a gidansa dake Tudun Wada a birnin Gombe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel