Muddin Aka Yi Amfani da Sojoji a Nijar, A Shiryawa Yaƙi - Sojojin B/Faso da Mali

Muddin Aka Yi Amfani da Sojoji a Nijar, A Shiryawa Yaƙi - Sojojin B/Faso da Mali

  • Kasashen Burkina Faso da Mali duka su na goyon bayan kifar da mulkin farar hula a Jamhuriyyar Nijar
  • Gwamnatocin sojojin kasashen Afrikan ba za su yarda ECOWAS ta yi yunkurin dawo da Mohammed Bazoum ba
  • Sojojin sun fitar da sanarwar hadaka cewa za a tsokano su yaki idan dai aka yi amfani da karfi a kasar Nijar

Niger - A farkon makon nan, gwamnatocin sojojin da ke mulki a kasashen Burkina Faso da Mali su kayi magana a kan abubuwan da ke faruwa a Nijar.

A rahoton da DW ta fitar, an ji cewa kasashen biyu su na goyon bayan gwamnatin sojan da aka kafa a Nijar a sakamakon kifar da Mohammed Bazoum.

Takwarorin Janar Abdourahamane Tiani a yammacin Afrikan sun nuna ba za su bari ayi amfani da karfin bindiga wajen karbe mulki a Jamhuriyyar ba.

Kara karanta wannan

Dole Bazoum Ya Koma Mulki, Gwamnatin Amurka Ta Goyi Bayan Tinubu da ECOWAS

Sojoji
Kanal Mamady Doumbouya da su kayi juyin mulki a Guinea Hoto; Getty Images
Asali: Getty Images

Jawabin Kasashen Burkina da Mali

“Duk wani tsoma bakin sojoji a Nijar zai zama tamkar buga gangar yaki da Burkina Faso da Mali”

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Mummunan tasirin yin amfani da sojoji a Nijar shi ne…za a rugurguza daukacin yankin. Kuma gwamnatocin biyu ba za su yi amfani da haramtacce, mara imanin takunkumi da ya saba doka a kan mutane da hukumomin Nijar ba."

- Kanal Abdoulaye Maïga

A jawabin hadakar da gwamnatocin su ka fitar, za a iya cewa sun yi raddi ga kungiyar ECOWAS mai tunanin aiki da soji a dawo da farar hula.

Rahoto ya ce martani ne ga kungiyar ECOWAS ta kasashen yammacin Afrika a karkashin jagorancin Bola Tinubu da ta ke gargadin sojojin Nijar.

Gwamnatin Guinea wanda aka samar ta hanyar kifar da farar hula, tayi tir da matakin da ECOWAS ta dauka na kakabawa kasar takunkumi.

Kara karanta wannan

Ta Rikice a Nijar, Masu Zanga-Zanga Sun Farmaki Ofishin Jakadancin Faransa

Ana cafke jagororin PNDS

A wani rahoto daga Reuters, an ji yadda sojojin da su ka hambarar da mulki su ke cafke manyan jagororin jam’iyyar PNDS mai-mulki a jamhuriyyar.

Kakakin jam’iyyar ta PNDS, Hamid N'Gade ya shaida cewa an tsare wasu Ministocin tarayya biyu; Mahamane Sani Mahamdou da Ousseini Hadizatou.

Haka zalika shugaban jam’iyyar, Foumakoye Gado ya na daure a hannun masu juyin mulki. Wannan lamari ya jawo kungiyar EU ta na mai Allah-wadai.

Janar Abdourahamane Tiani

Labari ya zo cewa shugaban sojojin fadar shugaban Nijar, Janar Abdourahamane Tiani ya ci amanar Mohammed Bazoum, ya kifar da gwamnatinsa.

A baya Janar Tchiani ya ruguza yunƙurin juyin mulki har sau biyu a Jamhuriyar Nijar, wannan karo sai ya jagoranci hambarar da mulkin farar hulan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng