Labaran garkuwa da mutane
Miyagun da suka yi garkuwa da shugaban jam'iyyar PDP na jihar Legas da wasu kusoshin jam'iyyar sun buƙaci a ba su N200m a matsayin kudin fansar sako su.
Tsagerun ƴan bindiga sun yi awon gaba da shugaban hukumar kula da tashohin manyan motoci na jihar Oyo, Alhaji Akeem Akintola, maharan sun shiga har gidansa.
Wasu miyagun yan bindiga da suka sace mutum 31 a jihar Katsina sun aike da sako kudin fansan da za a ba su kafin su sako mutanen da suka sace a jihar.
An gargadi Shugaban kasa Bola Tinubu kan tashin hankalin da zai dabaibaye gwamnatinsa a sabon hasashen da Primate Elijah Ayodele ya saki bayan sace shugaban PDP.
Yan bindiga sun sace mataimakin VC na jami'ar jihar Abiya watau ABSU yayin da ya tsaya shan mai a wani gidan mai tare da mai ɗakinsa, babu wani bayani har yanzu.
Rahotanni sun nuna cewa wasu da ba a san ko su waye ba sun yi awon gaba da shugaban jam'iyyar PDP na jihar Legas a titin zuwa Ibadan jiya Alhamis da yammaci.
Wasu gwamnoni akalla 9 a Najeriya sun tabbatar da aniyarsu ta zartar da hukuncin kisa ko ɗaurin rai da rai kan duk wanda aka kama da laifin garkuwa da mutane.
Jami'ar Bayero da ke Kano ta musanta rahoton da ake yaɗawa cewa an yi garkuwa da mutane a harabar jami'ar da ke cikin birnin Kano, ta ce labarin kanzon kurege ne.
Yan sanda sun kama mata da miji da suka yi karyar an yi garkuwa da su don su samu kudin fansa har naira miliyan biyar da nufin sayen gida a Badagry da ke Legas.
Labaran garkuwa da mutane
Samu kari