‘Yan Bindiga Sun Kuma Ta’adi a Abuja, An Yi Garkuwa da Mace da Yaranta Har da Jariri

‘Yan Bindiga Sun Kuma Ta’adi a Abuja, An Yi Garkuwa da Mace da Yaranta Har da Jariri

  • A lokacin da gwamnatin tarayya ta ke ikirarin samar da ingantaccen tsaro, an sake sace mutane a Abuja
  • Wasu ‘yan bindiga sun shiga unguwar Zone 5, sun yi nasarar yin awon gaba da wata mata da ‘ya ‘yanta
  • A cikin wadanda yanzu ake tsoron cewa sun shiga hannun miyagun, har da wani jaririn da ake goye da shi

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - ‘Yan bindiga sun kai hari a unguwar Zone 5 da ke yankin gidajen da ke rukunin Kubwa a birnin tarayya Abuja.

Rahoton da Punch ta fitar da safiyar Litinin ya ce ‘yan bindigan sun yi awon gaba da wata da ‘ya ‘yanta a mummunan harin.

Abuja
‘Yan bindiga sun shiga Abuja Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Daga ciki ‘ya ‘ya uku na wannan mata da ake zargin an yi garkuwa da su, har da jairirinta mai watanni shida a duniya.

Kara karanta wannan

"Yan sanda sun yi garkuwa da ni, sun karbi Naira miliyan 1 kudin fansa", cewar Mr Soyemi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan bindiga sun zo Abuja cikin dare

Majiya ta shaida cewa ‘yan bindigan sun duro titin Arab da ke birnin tarayya Abuja ne jim kadan bayan an yi sallar Isha’i.

Abin ya faru ne da kimanin tsakanin karfe 8:00 zuwa 9:00 na dare a ranar Lahadi, daga nan su ka shiga bude wata ko ina.

Wannan ya faru ne a lokacin da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta ke kokarin kawo karshen garkuwa da mutane da ake yi.

Rahoto ya zo cewa an tashi wani kauye sakamakon hare-haren 'yan bindiga a Abuja.

Wasu miyagu su kan dauke mutane su boye a jeji domin ganin an biya su kudin fansa, har ta kai sarakuna ba su tsira ba.

'Yan bindiga sun addabi Zone 5 a Abuja

Wani mazaunin unguwar ya zanta da ‘yan jarida a boye, ya shaida masu cewa garkuwa da mutane ta fara yawa a yankin.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya tono adadin bashin aikin titunan da Shugaba Buhari ya tafi ya bari

"A duk Disamba, garkuwa da mutane ya zama ruwan dare a nan, idan za ku iya tuna abin da ya faru a Disamban bara."

- Mazaunin Abuja

An yi irin haka a shekarar da ta wuce, wannan karo abin da ya sake faruwa, hakan ya tada hankalin mazauna yankin sosai.

Gwamna ya bi 'yan bindiga a Katsina

Rahoto ya zo cewa Dikko Umaru Radda yana cikin tawagar sojoji da ta shiga jejin Zakka a Safana domin hana a kawo hari.

Mai girma Gwamnan jihar Katsina ya yi ta-maza, ya bar ayyukan da yake yi domin aukawa miyagun da ke ta'azi a jejin Zakka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel