Labaran garkuwa da mutane
Tsofaffin sojoji sun taimakawa gwamnatin Bola Tinubu da shawarwarin magance matsalar tsaro, ana sai a samu zaman lafiya a 2024 idan aka dauki maganarsu.
Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindiga sun sako basaraken Abuja da mukarrabansa guda 5 bayan biyan kudin fansa har naira miliyan takwas, tabar wiwi, barasa da kati.
Iyalan Nabeeha Al-Kadriyar sun bayyana cewa suna cikin tashin hankali yayin da suke jiran kiran yan bindigar da suka sace yaransu bayan cikar wa'adin da suka basu.
Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindiga sun shiga wani kauyen karamar hukumar Sabon Gari da ke jihar Kaduna, sun sace uwa da ɗanta, amma mijin ya tsere.
Rundunar yan sandan jihar Kwara ta bayyana cewa jami'an tsaron haɗin guiwa sun yi nasarar kama mutum 3 da ake zargi da hannu a sace basarake da wasu uku.
'Yan bindiga sun kashe wani magidanci mai suna Tijani Amedu tare da yin garkuwa da kananan yara 13 a hanyar Kaduna, kuma sun nemi kudin fansa naira miliyan 60.
Doka ta haramta tara kudi a biya ‘yan bindiga a Najeriya. Muhammad Badaru Abubakar ya ce idan ana biyan fansa, ‘yan bindiga ba za su daina ta’adi a Najeriya ba.
Ministan Tsaron Najeriya, Badaru Abubakar ya gargadi 'yan Najeriya kan biyan kudaden fansa ga 'yan bindiga inda ya ce hakan kara lamarin zai yi a kasar.
Rahotanni daga iyalan shugaban ƙaramar hukumar Ukum ta jihar Benuwai wanda ke hannun masu garkuwa, sun nuna cewa maharan sun nemi kuɗin fansa N50m.
Labaran garkuwa da mutane
Samu kari