Kasashen Duniya
Wasu ‘Yan Sanda sun kama Edwin Congo a cikin farkon makon nan. An yi ram da shi ne bayan ya ajiye kwallon kafa ya shiga harkar shigo da miyagun kwayoyi a Sifen.
Asibitin Barchi yana yammacin Kabul ne, yankin da mabiya akidar Shi’an Hazara suka fi yawa, wadanda mayakan kungiyar ISIS ke yawan yi ma barazana da hare hare.
Mun kawo jerin wasu Jihohi da su ka samu fiye da Jakada guda a sababbin nade-naden da aka yi dazu. Delta, Ebonyi, da kuma Sokoto sun tashi babu ko mutum daya.
Shugaban kasar Liberia, George Weah ya sanar bude Masallatai da Coci-coci a kasar daga ranar Juma’a, 15 ga watan Mayu a kokarinsa na dakile cutar Coronavirus.
Wata Budurwa mai suna Nasro Ade da ta kamu da cutar COVID-19 a Ingila ta cika. Iyayen Ade sun yi sallama da ita ne ta wayar salula a lokacin da ta ke jinya.
Firai minista na kasar Lesotho, Mista Thomas Thabane dan shekara 80 ya jaddada aniyarsa ta yin murabus daga mukaminsa a karshen watan Yuli sakamakon tsufa.
Gwamnatin kasar Japan ta shirya sanar da maganin Remdesivir tare da kaddamar da fara amfani da shi a ranar Alhamis, 7 ga watan Mayu a matsayin maganin COVID19.
Duba matakan da hukumar ta shimfida domin a bi su wajen tantance limamai da ladanai kafin a zabo su su yi sallah da kiran sallah a masallatan Makkah da Madina
Yansandan birnin Ross Townna Amurk sun bayyana cewa an tsinci gawar Bing Liu a gidansa a ranar Asabar dauke da raunin bindiga a wuyansa, kan sa da kuma maransa.
Kasashen Duniya
Samu kari