Sin ta na yunkurin awon gaba da bayanan binciken COVID-19 – Amurka

Sin ta na yunkurin awon gaba da bayanan binciken COVID-19 – Amurka

- Hukumomin Amurka sun ce Mutanen kasar Sin su na kokarin yi masu kutse

- Amurka ta ce Sinawa na neman sace wasu bayanai a kan maganin COVID-19

- Ma’aikatar kasar wajen Sin ta ce zargin da ake yi mata sam ba gaskiya ba ne

Hukumomin kasar Amurka sun fito su na gargadi Duniya cewa kasar Sin ta na neman hanyar da za ta sace wasu bayanai a kan binciken da ake yi na gano maganin cutar COVID-19.

Jaridar Punch ta ce kasar Amurka ta bayyana wannan ne a ranar Laraba, 13 ga watan Mayu, 2020. Wannan bayani da Amurka ta yi a jiya ya sake hura wutan rikicinta da kasar ta Sin.

Hukumar FBI da wata hukuma a Amurka sun ce wasu Sinawa su na kokarin satar muhimman bayanai game da binciken magungunan COVID-19 da ake yi ta kafofin yanar gizo.

A cewar hukumomin na Amurka, binciken da su ke yi wajen samo maganin da zai iya kashe cutar Coronavirus a Duniya ya na fuskantar barazana sosai daga mutanen kasar Sin.

KU KARANTA: Amurka ta yi wa Najeriya sabon alkawarin gudumuwar COVID-19

Sin ta na yunkurin awon gaba da bayanan binciken COVID-19 – Amurka
Shugaban kasar Sin Xi Jinping Hoto: VOA
Asali: Getty Images

Masu yin kutse a yanar gizo daga Sin su na neman hanyar sace wasu bayanan ilmi na nazari da binciken da Amurka ta ke yi kan wannan cuta da binciken nemo maganin da ake yi.

Jawabin ya ce: “Yunkurin kutsen da Sin ta ke yi na kai wa wadannan bayanai hari ya jefa kokarin da kasar mu ta ke yi wajen kawo karshen annobar cutar COVID-19 a cikin hadari.”

A jawabin na FBI da ‘yaruwarta mai kare shafukan yanar gizo daga hari, ba su bada wata hujja da ke tabbatar da cewa kasar Sin ta na neman yi mata kutse a cikin aikin da ta ke yi ba.

Dama can manyan kasashen Duniyar sun dade su na ta nunawa juna yatsa. Da aka tambayi Donald Trump a game da zargin, ya nuna sam ba ya jin dadin abin da Sin ta ke yi masu.

“Menene sabon abu game da Sin? Menene sabo? Fada mani. Ba ni farin ciki da kasar Sin.” Inji Trump. Kasar Sin ta bakin Zhao Lijian ta karyata hakan, ta ce ta yi nisa a bincikenta.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel