Yan bindiga sun bindige jarirai 2 da wasu mutane 11 a Asibitin Afghanistan

Yan bindiga sun bindige jarirai 2 da wasu mutane 11 a Asibitin Afghanistan

Akalla mutane 13 ne suka rigamu gidan gaskiya sakamakon wani hari da yan bindiga suka kai wani asibiti dake garin Kabul na kasar Afghanistan, daga ciki har da jarirai 2.

Kamfanin dillancin labaru na AFP ta ruwaito kakaakin ma’aikatan cikin gida, Tareeq Arian ne ya bayyana haka a ranar Talata, inda yace asibitin da aka kai harin na masu haihuwa ne.

KU KARANTA: Hukumar EFCC ta kama yan China 2 da laifin baiwa shugaban EFCC cin hancin N100m

Yan bindiga uku ne suka far ma asibitin, kuma suka rike asibitin tsawon sa’o’i kafin jami’an tsaro su samu nasarar kashe su duka, sa’annan suka tseratar da jariran dake cikin asibitin.

“Daga cikin wadanda suka mutu akwai mata masu shayarwa, ma’aikatan jinya, da kuma jarirai, mutane 15 sun jikkata, yayin da aka ceto fiye da mutane 100, har da yan kasar waje uku.” Inji Kakaaki Tareeq.

Yan bindiga sun bindige jarirai 2 da wasu mutane 11 a Asibitin Afghanistan

Asibitin Afghanistan Hoto: Punch
Source: UGC

Asibitin Barchi yana yammacin Kabul ne, yankin da mabiya akidar Shi’an Hazara suka fi yawa, wadanda mayakan kungiyar ISIS ke yawan yi ma barazana da hare hare.

Wani likitan yara da ya tsallake rijiya da baya ya ce ya ji karan fashe fashen bamabamai a bakin kofar shiga asibitin a lokacin da asibitin ke cike da likitoci da masu ganin likita.

Wannan asibiti yana samun kulawa ne daga likitocin duniya na Doctors Without Borders, don haka akwai likitocin kasashen waje da dama dake aiki a asibitin kyauta.

A jawabin mataimakin ministan lafiya na kasar, Waheed Majroh ya bayyana damuwarsa game da harin, sa’annan yayi kira ga bangarorin dake rikicin su daina kai ma asibiti da jami’an asibiti hari.

Jim kadan bayan wannan hari, kwatsam sai wani dan kunar bakin waje ya tashi wasu mutane 24 a yayin jana’izar wani dansanda da ya mutu a gabashin lardin Nangarhar.

Wani mutumi da ya jikkata a sanadiyyar harin, Amir Muhammad ya bayyana cewa dubun dubatan jama’a ne suka taru don jana’izar mamacin a lokacin da harin ya auku.

Sai dai kungiyar yan ta’addan Taliban ta musanta hannu cikin hare haren duka.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel