Jerin Jihohin da su ka samu fiye da Jakada guda a sababbin nade-naden da aka yi

Jerin Jihohin da su ka samu fiye da Jakada guda a sababbin nade-naden da aka yi

A yau Talata, 12 ga watan Mayu, 2020, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aikawa majalisar dattawa sunayen wasu wadanda ya zaba a matsayin jakadun Najeriya a kasashen waje.

Mai girma Muhammadu Buhari ya dogara ne da sashe na 171 na kundin tsarin mulki da ya ba shugaban kasa zaben jakadun Najeriya, inda su kuma sanatoci za su yi aikin tantancewa.

Legit.ng ta samu sunayen wadanda shugaban kasa Buhari ya zaba, daga ciki akwai jihohin da aka zakulo mutane biyu. Daga cikin wadannan jihohi har da jihar shugaban kasa ta Katsina.

1. Jihar Bayelsa

Jihar Bayelsa ta samu mutum biyu a cikin sunayen da shugaban kasar ya aikawa majalisa. Wadanda aka zaba daga Bayelsa su ne: S. Agbana da B.B.M. Okoyen.

2. Jihar Kuros-Riba

Kuros-Riba ta yi dace da mutane biyu a jerin zababbun jakakun Najeriya. Sunayen M.O. Abam da A.E. Allotey fadar shugaban kasa ta aikawa majalisar dattawa dazu.

3. Jihar Jigawa

Jiha ta uku da ta samu mutum fiye da guda a jerin jakadun da shugaba Muhammadu Buhari ya zaba ita ce Jigawa. M. S. Abubakar da Y. A. Ahmed ne su ka samu shiga.

4. Jihar Kano

Kano mai dinbin mutane a Najeriya ta samu mutane biyu a cikin jerin jakadun kasashen ketare. Wadanda aka zaba daga jihar Kano su ne A. Sule da kuma G. Y. Hamza.

KU KARANTA: Sunayen Jakadun da Shugaban kasa ya turawa Sanatocin Najeriya

Jerin Jihohin da su ka samu fiye da Jakada guda a sababbin nade-naden da aka yi
Shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da Jakadan kasar Jafan
Asali: Twitter

5. Jihar Katsina

A jihar Katsina, an zabi mutane biyu a matsayin jakadu: N. Rimi da kuma L. S. Ahmed-Remawa.

6. Jihar Kogi

Wata jihar da ta yi wannan dace ita ce Kogi inda aka aika sunayen I. R. Ocheni da I. A. Yusuf.

7. Jihar Neja

A Neja, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zabi A. A. Musa da N. A. Kolo a matsayin jakadu.

8. Jihar Osun

Jihar karshe da ke cikin wannan jeri ita ce Osun, wanda ita ce kadai ta dace a kasar Yarbawa inda aka turawa majalisar dattawan sunayen O. O. Aluko da kuma I. A. Alatishe.

A daidai wannan lokaci kuma babu sunan wani jakada daga jihohin Sokoto, Delta, Ebonyi da kuma jihar Ekiti. Watakila nan gaba a sake zakulo wasu sababbin jakadun.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng