Wasu Bayin Allah su na ji su na gani COVID-19 ta kashe ‘Yar su mai shekara 25

Wasu Bayin Allah su na ji su na gani COVID-19 ta kashe ‘Yar su mai shekara 25

- Wata Budurwa mai suna Nasro Ade da ta kamu da cutar COVID-19 a Ingila ta cika

- Iyayen Ade sun yi sallama da ita ne ta wayar salula a lokacin da ta ke cikin gargara

Mun samu labari cewa dole ta sa wasu mutane sun yi wa ‘diyarsu da ke kwance a kan gadon asibiti sallama ta wayar bidiyo bayan ta kamu da muguwar cutar Coronavirus.

Miss Nasro Ade mai shekaru 25 da haihuwa ta kamu da cutar COVID-19 wanda ya sa aka kwantar da ita a asibitin St George da ke garin Tooting a birnin Landan, a kasar Birtaniya.

Likitoci sun killace Ade ne a wannan asibiti da ke kudancin Landan a Ingila bayan gwaji ya nuna cewa ta na cikin mutane 200, 000 da ke dauke da kwayar Coronavirus a Ingila.

A karshe iyayen Nasro Ade sun yi bankwana da ita ne ta kafar FaceTime a lokacin da ajali ya bijiro mata. Ade ta cika ne bayan ta yi ta fama da jinya na tsawon kwanaki 11.

KU KARANTA: Abin da ya sa Gwamnan Bauchi ya ce a rika amfani da Chloroquine

Iyayen marigayiyar sun dauko wayarsu na iPhone su ka yi sallama da yarinyar ta su yayin da ta ke daf da busa numfashin karshe. A karshe Ade ta ce ga garinku nan a ranar Talata.

Wata kawar Ade mai suna Isha Ceesay, ta bayyana cewa sun yi takaicin yadda mutuwa ta dauke abokiyar ta su ba tare da sun samu damar rungume ta lokacin da ta ke gargara ba.

“Likitoci da malaman jinyan su ka kawo shawarar ta yi bankwana da iyayenta saboda ba su da tabbacin ta na da sauran kwana – domin ciwonta ya daina jin wani magani.”

Isha ta ke bayyanawa jaridar Telegraph yadda kawarta ta yi ganawar karshe da iyayenta kafin ta cika. Rahotanni sun ce marigayiyar ta yi ta fama da mugun ciwon koda a asibitin.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng