Ji ka karu: Tsare tsaren da Saudiyya take bi wajen zaben Limaman masallacin Annabi
Hukumar dake kula da manyan masallatan Musulunci dake birnin Makkah da Madina a kasar Saudiyya tana da tsari na musamman da take bi wajen zaben Limamai da Ladanan Masallatan.
BBC Hausa ta ruwaito tsare tsare da matakan da hukumar ta shimfida domin a bi su wajen tantance limamai da ladanai kafin a zabo su su yi sallah da kiran sallah a masallatan biyu.
KU KARATA: Ministan Buhari, Raji Fashola ya bayyana matakin da yake dauka na kariya daga Coronavirus
Ga sharuddan kamar haka;
- Dole ne masu takarar su kasance yan kasar Saudiyya
- Masu takarar Limanci ko Ladanci ba zasu gaza shekara 30 ba
- Dole ne masu takarar suna samu digiri na biyu daga daya daga cikin jami’o’in kasar
- Ladani sai ya kasance yana da sani sosai game da kiran Sallah daga Qur’ani da Hadisi
- Dole ne masu takarar su kasancu masu zazzakar murya da iya rera karatu
- Limami dole ne ya kasance mahaddacin Qur’ani
- Limami dole ne ya kasance ya kware a tajweedin Al-Qur’ani
Idan aka kammala tantancewa daga cikin masu muradin Limanci ko Ladanci a masallatan biyu, sai kuma a zarce mataki na gaba inda majalisar zartarwa za ta amince da su.
Sai dai majalisar za ta amince da su ne kadai bayan samun shawara daga bakin shugaban kula da Masallatan biyu, a yanzu dai Sheikh Abdulrahman Sudais ne shugaban majalisar.
Daga karshe duk wanda ya samu nasarar zama limami ko ladani, za’a kayyade masa wa’adin shekara hudu don gudanar da aikinsa, amma akwai daman sabunta wa’adin nasu.
A wani labari kuma, Dan tsohon shugaban kasa marigayi Umaru Musa Yar’adua, Musa ya tuna da mahaifinsa bayan shekaru 10 da rasuwa, da wasu kyawawan addu’o’i daga cikin Al-Qur’ani.
A ranar 5 ga watan Mayun shekarar 2010 ne Yar’adua ya rasu bayan fama da matsananciyar rashin lafiya, koda yake dai kafin rasuwar ya sha fama da ciwo, inda yayi jinya a Saudiyya.
Biyo bayan rasuwar sa a wani halin sarkakiya ne mataimakin, Goodluck Ebele Jonathan ya dare madafan iko, kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ta tanada.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng