Yanzu babu wani Mutum mai cutar COVID-19 a kasar Mauritius – Jami’ai

Yanzu babu wani Mutum mai cutar COVID-19 a kasar Mauritius – Jami’ai

- Rahotanni su na yawo cewa masu dauke da COVID-19 a Mauritius sun warke

- A yanzu babu wani wanda ya ke kwance ya na faman jinyar cutar a cikin kasar

- Mauritius ta bi sahun Lesotho inda a nan ma babu labarin mai dauke da cutar

Kasar Mauritius ta bayyana cewa gaba daya wadanda su ka kamu da cutar COVID-19 sun warke. A halin yanzu babu wani mai fama da wannan cuta a cikin kasar Afrikar.

Mauritius ta shiga cikin jerin kasashen da yanzu babu mai jinyar Coronavirus. Daga lokacin da annobar ta barke zuwa yanzu, mutane kusan 70,000 su ka kamu a Afrika.

Har a zuwa jiya 12 ga watan Mayu, 2020, Lesotho ce kawai kasar da COVID-19 ba ta ratsa ba a Afrika. Kasashen Eritrea, Seychelles da Mauritania su na da mai jinya daya.

Kasar ta Mauritius ta ce yanzu kowa ya warke daga cikin mutane 322 da su ka kamu da cutar kwanaki. Mummunar cuta ta yi sanadiyyar mutuwar mutanen kasar goma.

KU KARANTA: Buhari ya zama gwarzon yaki da Coronavirus a Nahiyar Afrika

Wannan labari ya na nufin akwai wannan cuta a cikin kasashe 52 na nahiyar Afrika. Coronavirus ta kashe mutane kusan 2, 400 a kasashen Afrika a cikin watanni kusan biyar.

Ga wadanda ba su da labari, Mauritius karamar kasa ce cikin tsibiri zagaye da teku kusa da yankin kudu maso gabashin nahiyar. Akwai kimanin mutane miliyan 1.2 a kasar.

A ranar 11 ga watan Mayu, aka shafe rana ta biyar a jere da ba a samu bullar COVID-19 ba. Ko da babu wanda kwayar cutar ta harba, gwamnati ta ba ta bada damar fita ba tukuna.

A farkon makon nan ne ma’aikatar kiwon lafiya ta Mauritius ta ce ta yi wa mutane har 73, 572 gwaji. Ana yi wa mutane gwajin PCR ne da na 'Rapid Antigen' a asibitocin kasar.

Gwamnati ce ta ke daukar nauyin kula da ‘yan kasar Mauritius, duk wani ainihin ‘dan kasar zai iya sayen magani a duk shagon da ya ga dama ba tare da biyan ko sisin kobo ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel