Kallo ya koma sama: Dan bindiga ya halaka mutumin dake binciken maganin Coronavirus

Kallo ya koma sama: Dan bindiga ya halaka mutumin dake binciken maganin Coronavirus

A wani lamari mai daure kai, wani dan bindiga da ba’a san ko wanene ba ya bindiga wani babban masanin kimiyya da fasaha dake binciken maganin Coronavirus a kasar Amurka.

Gidan talabijin na CNN ta bayyana cewa suna masanin da aka kashe Bing Liu dan shekara 37, kuma mukaminsa shi ne mataimakin Farfesa a jami’ar Pittsburg ta kasar Amurka.

KU KARANTA: Sanatoci sun shawarci Buhari game da yadda ya kamata ya sauya aikin Yansanda

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Bing Liu ya yi nisa sosai a binciken da yake yi na samo maganin annobar Coronavirus, an kashe shi ne a gidansa a karshen makon data gabata.

Yansandan garin Ross Town sun bayyana cewa an tsinci gawar Bing Liu a gidansa a ranar Asabar dauke da raunin bindiga a wuyansa, kan sa da kuma maransa.

Kallo ya koma sama: Dan bindiga ya halaka mutumin dake binciken maganin Coronavirus
Bing Liu Hoto: Documentary Org
Asali: UGC

Sai dai Yansandan sun ce alamu sun nuna an kashe Liu ne a harin dan bindiga, amma dai sun nesanta kisan ga nuna wariyar cewa shi dan kasar China ne ba dan kasar Amurka ba.

Haka zalika Yansandan sun gano mutumin da suke sa ran shi ya kashe Liu a cikin motar Liu din, amma shi ma ya kashe kansa ta hanyar dirka ma kansa harsashi a kai.

Wannan lamari ya yi matukar tayar da hankulan jama’a ganin cewa Liu yana neman maganin COVID-19 ne a daidai lokacin da aka kashe shi, don haka ake tunanin da walakin goro a miya.

Abokan aikinsa sun bayyana shi a matsayin kwararren masanin kimiyya, kwararren bincike, don haka sun yi alkawarin karkare binciken maganin da yake yi don karrama shi.

“Mun kadu da mutuwar Bing Liu, kwararren mai bincike a jami’ar Pitts. Jami’ar na mika ta’aziyyarta ga iyalan Liu, abokai da abokan aikin sa, Bing na gab da binciko maganin COVID19, za mu cigaba da binciken da yake yi don karrama shi.” Inji shi.

A wani labarin kuma, hukumar kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta sanar da shirinta na yi ma yan wasan gwajin cutar Coronavirus domin tabbatar da matsayin lafiyar yan wasan.

Matakin na daga cikin sharuddan da aka gindaya ma kungiyoyin kasar Spaniya dake gasar La Liga yayin da ake shirin cigaba da karkare gasar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng