Jerin kasashe guda 10 da suka fi ko ina talauci a duniya a shekarar 2019

Jerin kasashe guda 10 da suka fi ko ina talauci a duniya a shekarar 2019

- Idan aka ce kasashen da suka fi talauci a duniya ana nufin kasashen da suka sha fama da rikici irinsu rikicin kabilan dana addini, yunwa da kuma matsalar canjin yanayi

- Yanzu dai zamu yi la'akari akan kasashe guda goma da suka fi kowanne kasashe talauci a duniya

Ba abin mamaki bane kasashen da zamu lissafo, duba da yadda suka sha fama da matsaloli irin su cututtuka, yake-yake, rikicin kabilanci da addini, matsalar canjin yanayi da dai sauransu. Wadannan matsaloli suna makasudin sanya kasashe cikin bakin talauci da yunwa.

Yanzu dai ga jarin kasashen guda goma za mu kawo muku.

10. Mozambique

Mozambique kasashe da Allah yayi mata arzikin ma'adanai, kuma yanzu haka tana daya daga cikin kasashen Afrika da arzikin su yake farfadowa. Sai duk da haka har yanzu kasar tana farfadowa daga matsalar da ta shiga a shekaru 16 da suka gabata lokacin da aka yi yakin basasa, bayan samun 'yancin kai daga kasar Portugal daga shekarar 1975 zuwa 1992.

9. Liberia

Kasar Liberia ita ce jamhuriyyar da tafi kowacce jimawa a nahiyar Afrika, tayi fama da yakin basasa tsakanin shekarar 1989 zuwa shekarar 2003. Yanzu da komai ya dawo daidai a kasar, har yanzu suna fama da matsanancin talauci sanadiyyar wannan yaki da ya faru. Haka kuma kasar ta Liberia ta sha fama da matsalar cutar nan ta Ebola wacce ta bulla a kasar a shekarar 2014 zuwa 2016.

8. Mali

Kasar Mali ita ce kasa ta hudu da tafi girma a nahiyar Afrika, babban birnin kasa na Timbuktu ya taba zama cibiyar kasuwanci a shekarun baya. Yanzu haka kasar wacce ta samu 'yancin kai daga wajen kasar Faransa a shekarar 1960 ta fara farfadowa daga bakin talaucin da take ciki.

7. Burkina Faso

Kasar Burkina Faso ta yi iyaka da kasar Mali da kuma kasar Niger, kasar Burkina Faso ita ma kasar Faransa ce ta raineta inda ta sha fama da matsaloli na juyin mulki da yake-yaken cikin gida bayan samun 'yancin kai a shekarar 1960.

6. Sierra Leone

Majalisar dinkin duniya ta taimakawa kasar Sierra Leone wacce ta sha fama da yakin basasa na tsawon shekara goma sha daya a shekarar 2002. Yanzu da kasar take farfadowa daga matsalar talauci, kasar tana daya daga cikin kasashen da suka sha fama da matsalar Ebola a shekarar 2014 zuwa 2016 tare da kasar Liberia.

KU KARANTA: Kullu Nafsin Za'ikatul Maut: Maciji ya hallaka wani dalibi a jami'ar jihar Bauchi

5. Burundi

Kasar Burundi tana fama da matsalar rikice-rikice tun daga lokacin da ta samu 'yancin kai a shekarar 1962 daga wajen kasar Belgium. Fadawar su yakin basasa a shekarar 1994 ya bar kusan kimanin kashi 65 cikin dari na al'ummar kasar cikin bakin talauci.

4. Chad

Duk da bututun mai na dala biliyan hudu da ya shiga ta kasar, Chadi ta na daya daga cikin manyan kasashen da suka fi ko ina talauci a kasar, kasar na fama da matsalar rashin abubuwan more rayuwa, sannan kuma ga matsalar 'yan ta'addar Boko Haram da ake fama da ita a yankin, haka kuma kasar na fama da matsalar canjin yanayi wanda ya sanya kusan kashi 48 cikin dari na al'ummar kasar cikin bakin talauci.

3. South Sudan

Jamhuriyar Sudan ta Kudu ta samu 'yancin kai a watan Yulin shekarar 2011, amma sun sha fama da matsalar rikice-rikice na tsawon lokaci. A shekarar 2016, bankin duniya ya bayyana cewa kusan kimanin kashi 82 cikin dari ne ke fama da matsanancin talauci a kasar.

2. Kasar Afrika ta Tsakiya

Babu mamaki dan ance kasar da tafi ko ina yunwa a duniya ta zama kasar da tafi ko ina talauci a duniya. A shekarar 2018 kasar Afrika ta Tsakiya ita ce kasar da aka bayyana a matsayin kasar da take fama da matsananciyar yunwa.

1. Niger

Ana tunanin cewa mutane a kasar Nijar basa wuce shekara 60.4 a duniya hakan ya sanya kasar ta zamo ta daya a cikin kasashen da suka fi talauci a duniya. Wani rahoto da bankin duniya ya fitar a shekarar 2014 ya bayyana cewa kimanin kashe 44.5 cikin dari ne suke fama da bakin talauci a kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel