Yan fashi sun kai ma wani babban dan kwallon duniya hari, sun kwashi gwala-gwalai

Yan fashi sun kai ma wani babban dan kwallon duniya hari, sun kwashi gwala-gwalai

Wasu miyagun yan fashi da makami dauke da wukake sun kutsa kai har cikin gidan dan wasan kwallon kafa na kungiyar Tottenham, Dele Alli, inda suka kwashe masa gwala-gwalai.

Kamfanin dillancin labaru na AFP ta ruwaito sai da yan fashin suka bazar da Dele Alli a kasa kafin suka fara binciken kayan da suke neman sacewa, sai dai ya sha ba tare da rauni ba.

KU KARANTA: Tinubu ya yi tsokaci game da nadin da Buhari ya yi ma Ibrahim Gambari

Dele dan shekara 24 dan asalin Najeriya, amma yana buga ma Ingila wasa ya kasance a gida ne tare da dan uwansa da kuma yan matansu a lokacin da barayin suka shiga.

Dele da sauran mutanen suna zaman killace kai a gida ne sakamakon ruruwar annobar Corona a kasar Ingila, tare da tsumayin kiran sa ya koma atisaye a kungiyar Tottenham.

Yan fashi sun kai ma wani babban dan kwallon duniya hari, sun kwashi gwala-gwalai

Dele Alli Hoto:SkySport
Source: UGC

A jawabinsa, Dele yace: “Nagode da sakonnin da kuka aiko min, lamari ne mai ban tsoro, amma a yanzu duk muna lafiya, mun gode da damuwa.” Kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Shi ma kakaakin Yansanda ya bayyana cewa: “Da misalin karfe 12:35 na daren Laraba 13 ga watan Mayu aka kira Yansanda cewa yan fashi sun shiga wani gida a Barnet.

“Maza biyu ne suka shiga gidan suka kwashe gwala gwalai da agoguna sa’annan suka tsere, daya daga cikin mazauna gidan ya samu rauni a fuskarsa bayan sun bige shi, amma raunin baya bukatan zuwa asibiti. Amma har yanzu bamu kama kowa ba.” Inji shi.

Dele zai fara atisaye da sauran yan wasan kungiyar Tottenham a mako mai zuwa ne a shirye shiryen cigaba da gasar Firimiya na kasar Ingila a wata mai zuwa.

A wani labari kuma, Kasar Saudi Arabia ta lissafa yan Najeriya 11,600 da suke makale a cikin kasarta saboda annobar Coronavirus, kuma ta fara shirin mayar dasu gida Najeriya.

Wani jami’in ofishin jakadancin Najeriya da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa Saudiyya ta sanar da su wannan matakin tun makonni da suka gabata.

A cewar Saudiyya, akwai yan Najeriya da suka tafi a Umrah amma saboda Corona basu samu daman komawa gida ba sakamakon matakan da gwamnatin kasar ta dauka.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel