Amurka za ta lura da yadda Najeriya za ta kashe gudumuwar COVID-19 - Jakada

Amurka za ta lura da yadda Najeriya za ta kashe gudumuwar COVID-19 - Jakada

A ranar Laraba, 13 ga watan Mayu, 2020 kasar Amurka ta ce ta kashe fam Dala miliyan 32.8 domin taimakawa Najeriya wajen shawo kan annobar Coronavirus da ake fama da ita.

Mary Beth Leonard ta ke cewa daga lokacin da annobar cutar COVID-19 ta barke, Amurka ta ba Najeriya Dala miliyan 32, kuma ta ce za ta so a kashe wannan kudi ta hanyar da ta dace.

Jakadar Amurka a Najeriya, Mary Beth Leonard ta ce kasarta ta tsara yadda za ta lura da hanyar da Najeriya za ta bi wajen batar da tallafin kudin da aka ba ta domin yaki da COVID-19.

Da ta ke wata hira da ‘yan jarida a jiya, Beth Leonard ta ce Amurka ta warewa kasashen Afrika kudi fam Dala miliyan 237 a da nufin agazawa nahiyar wajen ganin bayan annobar nan.

Abin da gwamnatin Amurka ta kashe yanzu a fadin Duniya ya kai fam Biliyan 2.4. Idan aka yi lissafi a kudin Najeriya, Amurkar ta fitar da kusan Naira tiriliyan daya a ‘yan watanni.

KU KARANTA: IMF: Kasashen Afrika za su gamu da asarar Naira Tiriliyan 2020

Amurka za ta lura da yadda Najeriya za ta kashe gudumuwar COVID-19 - Jakada
Jakadar Amurka Mary Beth Leonard tare da Shugaba Buhari Hoto: PM News
Asali: Twitter

Kamar dai yadda ta saba da ke-ke-da-ke-ke, Jakadar ta ce Amurka za ta bi diddikin yadda kasashen Duniya za su yi amfani da wadannan kudi da aka ba su na yaki da Coronavirus.

Kasar Amurka za ta dauki wadannan matakai na bin kadin yadda ake batar da kudin ne domin ta hana jami’an gwamnati yin gaba da dukiyar da ya kamata ta yi wa dinbin jama’a amfani.

Bayan wannan tabbaci, kasar ta Amurka ta yi magana game da dauke mutanenta da ta ke yi daga Najeriya, ta ce ta yi hakan ne domin wadannan Bayin Allah su samu su gana da iyalansu.

Amurka ta ce ta ji dadin ganin irin matakan da gwamnatin Najeriya ta dauka na yakar annobar, don haka ta yi alkawarin sake taimakawa kasar da taimakon kudi da kuma kayan aiki.

Bayan na’urorin taimakawa numfashi da aka yi wa Najeriya alkawari, gwamnatin Amurka ta ce ta na yin ruwa da tsaki ta hukumomin USAID da CDS wajen ganin an taimakawa Najeriya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel