An samu shugaban kasan Afirka na farko da zai yi murabus saboda ‘yawan shekaru’

An samu shugaban kasan Afirka na farko da zai yi murabus saboda ‘yawan shekaru’

Firai ministan kasar Lesotho, Thomas Thabane dan shekara 80 ya nanata aniyarsa ta yin murabus daga mukaminsa a karshen watan Yuli sakamakon tsufa da ya ce ta kama shi.

Shugaba Thabane ya bayyana haka ne a ranar Alhamis, 7 ga watan Mayu inda yace watakila ma ba zai kai karshen watan Yuli ba kafin ya jefar da kwallon mangwaro don ya huta da kuda.

KU KARANTA: Najeriya za ta yi amfani da magungunan gargajiya don yaki da Corona – Ministan Lafiya

Kamfanin dillancin labaru AFP ta ruwaito Thabane ya yi shirin barin mulki ne duk da yiwuwar tuhumarsa da za’ayi sakamakon zarginsa da ake yi da hannu cikin kisan matarsa a 2017.

Wa'adin mulkin Thabane zai kare ne a shekarar 2022 amma matsin lamba daga ciki da wajen jam’iyyarsa ta sa zai hakura saboda zarginsa da aikata laifin kisan kai.

An samu shugaban kasan Afirka na farko da zai yi murabus saboda ‘yawan shekaru’
Thabane Hoto: Aljazeera
Asali: UGC

A makon da ta gabata, jam’iyyarsa ta All Basotho Convention Party ta yi fatali da bukatarsa ta bashi kariya daga fuskantar shari’a bayan ya sauka daga mulki.

“Ina so na kara jaddada shiri na na yin murabus daga mukamin Firai minista, na dade ina muradin yin murabus a ranar 31 ga wata Yulin shekarar 2020 ko kuma kafin nan, amma idan duk sharadin yin murabus din sun cika.

“Ra’ayin kashin kai na ne, saboda bana jin karfi a jikina sakamakon tsufa, gwamnati da jam’iyyar da nake jagoranta su zasu tsara yadda zan yi murabus tare da tabbatar da cigaba da samar da zaman lafiya a Lesotho, hadin kai, sulhu da farfado da tattalin arzikin kasar daga cutar COVID19.” Inji shi.

A watan Yunin 2017 aka bindige tsohuwar matar Thabane, Lipoleo a gaban gidanta a binrin Maseru yayin da suke tsaka da rikicin rabuwar aure.

Sai dai Yansanda sun ga lambar wayar Thabane a cikin sadarwar da aka yi a inda aka kashe matar, hakan tasa jam’iyyar adawa ta ABC ta nemi ya yi murabus.

Bugu da kari ana zargin sabuwar matar da ya aura bayan watanni 2 da kisan Lepoleo, Maesaiah Thabane da hannu cikin laifin kisan, kuma tuni aka mika ta gaban kotu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel