Najeriya da Kasashen Afrika za su yi asarar $200b saboda COVID-19 – Inji IMF

Najeriya da Kasashen Afrika za su yi asarar $200b saboda COVID-19 – Inji IMF

Hukumar da ke bada lamuni a Duniya watau IMF, ta ce Najeriya da sauran kasashen Sahara a Afrika za su yi asarar kimanin fam dala biliyan 200 a dalilin annobar cutar COVID-19.

IMF ta ce kasashen za su yi wannan asara ne zuwa karshen shekarar nan da ake ciki ta 2020. Kasashen za su yi wannan rashi ne daga cikin kudin-shigar da su ke samu inji hukumar.

Annobar Coronavirus da ta sa tattalin arzikin Duniya ya ke neman rugurgujewa ne zai jawowa Najeriya da kasashen da ta ke makwabta da ita wannan muguwar asara a shekarar bana.

A wani hasashe da IMF ta yi tun kwanaki, ta ce annobar COVID-19 za ta jefa tattalin arzikin kasashen Sahara cikin matsala, kuma tattalin kasashen yankin zai tsuke da 1.6% a 2020.

Ba a taba samun lokacin da karfin tattalin yankin Sahara zai jagwalgwale irin yanzu ba. Sai kuma ga rahotanni sun fito cewa bana kasashen za su yi rashi daga kudin da su ke sa ran samu.

KU KARANTA: Akwai yiwuwar COVID-19 ta harbi mutane 20, 000 a Jihar Najeriya

Najeriya da Kasashen Afrika za su yi asarar $200b saboda COVID-19 – Inji IMF
Hedikwatar Hukumar IMF. Hoto daga: Premium Times
Asali: UGC

A wani faifai da IMF ta fito da shi ta ce yankin nahiyar na fama da matsin tattali da na kiwon lafiya, wanda hakan za su jawo abubuwa su tabarbarewa irinsu Najeriya da na kusa da ita.

Jaridar Punch ta ce shugaban sashen binciken IMF na yankin Afrika, Papa N’Diaye ne ya bayyana wannan kamar yadda aka ji a wannan jawabi da aka fitar a shafin yanar gizon hukumar.

Ndiaye wanda ke jagorantar masu nazari a game da yankin, ya ce nan da zuwa karshen shekarar 2020, Najeriya da sauransu za su rasa fam Dala biliyan 200 daga abin da ake sa ran samu.

“Za a gamu da babbar asara daga wannan annoba. Mu na sa ran kudin da kasashe za su samu ya zama 4% kasa da abin da aka samu watanni shida da su ka shude.” Inji Papa Ndiaye.

Jami’in ya ce kasashe za su shiga matsi idan ba su iya shawo kan annobar ba. Ndiaye ya koka a kan bata lokacin da annobar ta jawo wajen dabbaka yarjejeniyar kasuwanci a yankin.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel