Japan za ta fara amfani da ‘Remdesivir’ a matsayin maganin Coronavirus

Japan za ta fara amfani da ‘Remdesivir’ a matsayin maganin Coronavirus

Gwamnatin kasar Japan ta shirya sanar da maganin Remdesivir tare da kaddamar da fara amfani da shi a ranar Alhamis, 7 ga watan Mayu a matsayin maganin cutar Coronavirus.

Kamfanin dillancin labaru na AFP ta ce shugaban Japan, Shinzo Abe a makon da ta gabata ya bayyana cewa a shirye yake ya amince da maganin wanda kamfanin kasar Amurka ta sarrafa.

KU KARANTA: Buhari ya yi ma mai martaba Sarkin Daura addu’ar samun lafiya

Gwamnatin ta bayyana baya ga amfani da Remdesivir wanda kamfanin Gilead ta sarrafa shi a matsayin maganin cutar, za ta amince da maganin Avigan ma a wannan watan.

Idan ta cimma haka, kasar Japan za ta zamto kasa ta biyu da ta fara amfani da Remdesvir bayan kasar Amurka ta fara amfani da shi a ranar Juma’ar da ta gabata.

Kakaakin ma’aikatar kiwon lafiyan kasar Japan, Yoshihide Suga ta bayyana cewa: “Idan har babu wani matsala, muna sa ran amincewa da shi a yau.”

Japan za ta fara amfani da ‘Remdesivir’ a matsayin maganin Coronavirus
Shinzo Abe Hoto: Channels TV
Asali: UGC

An samar da Remdesivir ne don maganin cutar Ebola, amma bayan gwaji a kan masu cutar Coronavirus ya nuna yana rage tsawon lokacin da ake dauka kafin a warke daga cutar.

Sai dai ba’a tabbatar da yanayin rage mace mace daga Coronavirus din ba, amma ana amfani da maganin Remdisivir ne ta hanyar tsira shi a jikin mutum daga allura.

Shi kuma maganin Avigan an samar da shi ne a kamfanin Fujifilm Toyama Chemical na kasar Japan, kuma za’a amince da shi idan har ya yi aiki a kan marasa lafiya guda 100.

Sunan maganin Avigan Favipiravir, kuma a shekarar 2014 aka amince da shi a Japan don maganin mura, musamman muran da basu da magani a kasar.

Don haka ma babu shi a kasuwa, sai dai a sarrafa shi, a rarraba shi idan gwamnatin Japan ta bayar da izini. Amma kwayarsa ake sha, kuma yana hana kwayar cutar COVID19 ninkuwa.

Sai dai yayin da ake gwajin Avigan, sakamakon gwajin ya nuna yana shafar da a cikin mahaifa, don haka ba’a baiwa mata masu juna biyu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel