Gwamnatin Saudiyya za ta sallami yan Najeriya 11,000 saboda Coronavirus

Gwamnatin Saudiyya za ta sallami yan Najeriya 11,000 saboda Coronavirus

Kasar Saudi Arabia ta lissafa yan Najeriya 11,600 da suke makale a cikin kasarta saboda annobar Coronavirus, kuma ta fara shirin mayar dasu gida Najeriya.

Premium Times ta ruwaito jami’in ofishin jakadancin Najeriya da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa Saudiyya ta sanar da su wannan matakin tun makonni da suka gabata.

KU KARANTA: Gwamnatin jahar Yobe ta bayyana abin da ya kashe mutane 471 a jahar

A cewar Saudiyya, akwai yan Najeriya da suka tafi Umrah amma saboda Corona basu samu daman komawa gida ba sakamakon matakan da gwamnatin kasar ta dauka.

A ranar 2 ga watan Maris ne aka samu bullar cutar Coronavirus a kasar Saudiyya, a dalilin haka kasar ta dauki tsauraran matakai na hana shige da fice a kasar, musamman ga makwabtanta.

Gwamnatin Saudiyya za ta sallami yan Najeriya 11,000 saboda Coronavirus

Kasar Saudiyya Hoto:Aramco Expats
Source: UGC

Shi ma ministan harkokin kasashen wajen Najeriya, Geoffrey Onyeama ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda yace matsalolin sufuri ne suka kawo tsaiko ga kokarin dawo da yan Najeriyan.

Onyeama ya bayyana haka ne yayin da kwamitin kar-ta-kwana na shugaban kasa dake yaki da Coronavirus take gabatar da jawabin halin da ake ciki a ranar Talata a Abuja.

Ministan yace da so samu ne, da tun makonni 2 da suka gabata wasu sun fara dawowa gida, amma babu isassun wuraren da za’a killace su tsawon kwanaki 14 idan ma sun dawo.

“Muna sane da wannan, tun a makon data gabata ya kamata su dawo, amma hakan bai yiwu ba saboda bamu shirya masa ba, kamar yadda kuka sani, muna da iya jama’an da zamu iya kulawa da su a lokaci guda.

“Sai likitoci sun kula dasu tsawon sati biyu, amma akwai iya kayyadaddun jami’an kiwon lafiyan da zasu iya kula dasu, kuma kamar yadda sakataren gwamnati ya fada, sai mun sallami wasu kafin mu kawo wasu.” Inji shi.

Sai dai, Saudiyya ta ce yan Najeriya 340 ne kacal suka nuna sha’awar komawa gida Najeriya, don haka take neman taimakon ofishin jakadancin Najeriya wajen binciko sauran 11,260.

Amma koda aka tuntubi kakaakin ofishin jakadancin Najeriya a Saudiyya, Muhamamd Aliyu game da lamarin sai yace ba shi da ikon yin magana.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel