Annobar Corona: Shugaban kasa zai bude Masallatai amma da sharadi a kasar Liberia

Annobar Corona: Shugaban kasa zai bude Masallatai amma da sharadi a kasar Liberia

Shugaban kasar Liberia, George Weah ya sanar bude Masallatai da Coci-coci a kasar daga ranar Juma’a, 15 ga watan Mayu a kokarinsa na dakile cutar Coronavirus.

Punch ta ruwaito shugaba Weah ya bayyana haka ne a ranar Juma’ar da ta gabata, inda zai bude wuraren Ibada, amma ya kara wa’adin dokar ta baci a Monrovia, babban birnin kasar.

KU KARANTA: Baturiya da ta taso daga kasar Amurka don ganin saurayinta a Najeriya ta mutu a Otal

Sai dai ko da ya ayyana bude wuraren Ibadan, ya gindaya sharadi guda daya, wanda shine dole ne limaman Masallatai da coci su tabbata kashi 25 na jama’a kadai za su halarta don ibada.

Ma’ana kada yawan jama’an da zasu halarci wuraren Ibadan su haura kashi 25 na girman wurin Ibadan, yace idan suka tabbatar da haka, don dabbaka tsarin hana cudanya da jama’a.

Haka zalika shugaban ya dakatar da shige da fice daga kasashe guda 15 tare da hana kowanne irin kasuwanci a kasar don kauce ma yaduwar cutar a tsakanin al’umma.

Annobar Corona: Shugaban kasa zai bude Masallatai amma da sharadi a kasar Liberia

George Weah Hoto: Punch
Source: UGC

Kasar Liberia na da mutane 199 da suka kamu da cutar Coronavirus, 20 sun mutu.

A shekarar 2014, cutar Ebola ta kashe mutane 4,800 a kasar da jama’anta basu wuce miliyan 4.8 ba.

A nan gida Najeriya, akwai kiraye kiraye daga bakunan jama’a, Malamai da kungiyoyin addinai akan bukatar bude wuraren ibada, musamman Masallatai.

Jama’a na wannan kiraye kiraye ne duba da cewa gwamnati na bude kasuwanni domin a yi siyayya, amma ba za ta bude Masallatai don jama’a su gudanar da addu’o’i ba.

A wani labarin kuma, Gwamnan jahar Bauchi, Sanata Bala Muhammad ya sanar da garkame wasu kananan hukumomi guda uku a jahar Bauchi sakamakon bullar annobar Coronavirus.

Daily Trust ta ruwaito gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Lahadi, 10 ga watan Mayu na shekarar 2020 inda yace ya rufe garuruwan Katagum, Giade da kuma Zaki.

Bala ya danganta wannan mataki da ya dauka ga rahotannin da aka samu na mace mace a kananan hukumomin da kuma yaduwar cutar Coronavirus a cikinsu.

A dalilin yaduwar cutar da aka samu a kananan hukumomin Zaki, Giade da Katagum, adadin masu cutar Coronavirus a jahar Bauchi ya yi tashin gwauron zabi zuwa 181.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel