Jami’an tsaro sun kama Edwin Congo da zargin dillacin hodar iblis a Sifen

Jami’an tsaro sun kama Edwin Congo da zargin dillacin hodar iblis a Sifen

- ‘Yan Sandan Sifen sun kama Edwin Congo a cikin farkon makon nan

- An kama tsohon ‘Dan kwallon ne da laifin safarar munanan kwayoyi

A ranar Talata, 12 ga watan Mayu, 2020, jami’ai su ka kama wani tsohon ‘dan wasan gaban Real Madrid, Edwin Congo tare da wasu mutane da zargin su na safarar miyagun kwayoyi.

Kamar yadda mu ka samu labari daga jaridar Marca ta kasar waje, ‘yan sanda sun yi ram da tsohon ‘dan kwallon ne bayan wani samame da su ka kai a wani gari da ke kasar Sifen.

Jami’an tsaron sun saki wannan Bawan Allah bayan ya amsa wasu tambayoyi. Jaridar ta ce an tsare Edwin Congo mai shekaru 43 a ofishin hukumar da ke sa ido kan shan kwayoyi.

Ana zargin wannan mutumi ‘dan ainihin kasar Kolumbiya tare da wasu su 10 da hannu wajen safarar hodar iblis. Kasashe da-dama sun haramta amfani ko ciniki da wannan kwaya.

A halin yanzu dai Congo ya bar hannun jami’an tsaro tun bayan da ya yi jawabi a ofishin hukumar kasa. Alkaluma sun tabbatar cewa Sifen ce kasar da ta fi kowace bankado hodar iblis.

KU KARANTA: Wenger ya kama sunan 'Dan wasan da zai gaji kujerar Messi da Ronaldo

Congo wanda ya fara zuwa Sifen shekaru fiye da 20 da su ka wuce ya na zaune a kasar har gobe. Legit.ng ta fahimci cewa Congo ya fito ne daga babban birnin Columbia watau Bagota.

Kawo yanzu babu tabbacin ko hukumar kasar ta na gudanar da bincike a kan tsohon ‘dan wasan kwallon kafan. Hukumomin kasar Sifen ba su fitar da jawabi a game da lamarin ba.

A shekarar 1999, Congo ya shiga tarihin Duniya inda ya zama ‘dan kwallon da ya fi kowane tsada a tarihin kasar Kolumbiya bayan kungiyar Real Madrid ta saye sa daga Once Caldas.

Har ‘dan wasa Congo ya bar Real Madrid bai taba bugawa kungiyar ba, inda aka bada shi aro zuwa Valladolid. A karshe ya koma wasa irinsu Levante, Sporting Gijon da kuma Recreativo.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel