Jihar Kaduna
Malam Uba Sani ya ziyarci shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu domin ƙara jan hankalin gwamnatin tarayya ta taimaka wa jiharsa a fannin noma, lafiya da tsaro.
Wasu miyagun ƴan bindiga sun tare hanya a jihar Kaduna inda suka yi garkuwa da mutane masu yawa. Cikin waɗanda ƴan bindigan suka sace har mai shayarwa.
Tsagerun 'yan bindiga sun halaka jami'in rundunar mafarauta yayin da suka fita sintiri a kan titin Birnin Gwari, sun kuma kashe direbobin motocin haya biyu.
Wasu miyagun 'yan bindiga sun kai farmaki kan wani Masallaci a yankin Birnin Gwari da ke jihar Kaduna, sun halaka Liman da wani masallaci ɗaya ranar Talata.
Rahotanni sun kawo cewa hukumar da ke kula da tabbatar da ingancin Makarantun Jihar Kaduna (KSSQAA), ta rufe makarantar Al-azhar da ke Zaria kan zargin kisan dalibi.
Malamim addinin Musulunci, Sheikh Ahmed Gumi ya bude asusun ba da taimako don 'yan Falasdinu yayin da ake ci gaba da gwabza yaki tsakanin Isra'ila da Hamas.
Daga karshe dai an yi wa marigayi magajin garin Zazzau gatan da ake wa kowane Musulmi idan kwanansa ya ƙare, an masa Sallah kuma an kai shi makwanci.
A yau aka wayi gari da rasuwar jakadan Najeriya a ƙasar Morocco kuma Magajin Garin Zazzau, Alhaji Mansur Nuhu Bamalli, wanda Allah ya yi wa rasuwa a jihar Legas.
Alhaji Mansur Nuhu Bamalli, jakadan Najeriya a ƙasar Morocco kuma ɗan uwa na jini watau ƙanin mai martaba Sarkin Zazzau ya rasu yana da shekaru 42 a duniya.
Jihar Kaduna
Samu kari