Jihar Kano
Bayanan takardun shari’ar Abba v Gawuna ba kuskure ba ne a ra'ayin wasu. Chidi Odinkalu ya fadawa duniya cewa kotun daukaka kara ba za ta iya yin kwaba ta gyara ba.
Femi Falana, babban lauyan Najeriya, ya ce sabanin tunanin jama’a, kotun daukaka kara reshen Abuja, ba ta soke zaben gwamna Yusuf na jihar Kano ba.
Kingsley Chiedu Moghalu ya nuna hukuncin zaben Gwamnan Kano ya na neman tada zaune tsaye a sakamakon tsige Abba Kabir Yusuf, an ji yana kukan hukumomi sun lalace.
Labari ya zo daga Kwamishinan 'yan sandan jihar Kano cewa Jami’an tsaro sun damke wasu mutane da ake zargin sun fito yin zanga-zanga saboda hukuncin zaben gwamna.
Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya sake mika kasafin naira biliyan 24 don neman amincewar Majalisar yayin da ya himmatu wurin ayyyukan raya kasa a jihar.
Magoya bayan jam’iyyar NNPP sun fito kan titunan jihar Kano domin nuna adawa da rashin nasarar Gwamna Abba Yusuf a kotun daukaka kara. Yusuf jigon NNPP ne.
A yanzu wasu magoya bayan NNPP suna murnar kotun daukaka kara ta ba su gaskiya wajen rubuta hukuncin shari’ar Kano, amma lauyoyi sun ce ba haka abin yake ba.
Jam’iyyar APC ta yi ikirarin cewa sabon kwafin takardar CTC na hukuncin kotun daukaka kara kan shari'ar Kano kuskure ne na rubutu da kotu za ta gyara.
Jam’iyyar NNPP ta bukaci majalisar alkalai ta kasa da ta binciki sabani da aka samu a takardar CTC da kotun daukaka kara ta saki kan shari’ar zaben gwamnan Kano.
Jihar Kano
Samu kari