Yan sansanin IDP
Gobara a sanyin safiyar ranar Laraba ta yi sanadin mutuwar 'yan gudun hijira biyu tare da kona sama da gidaje 1,000, hukumar SEMA ta bayyana hakan.
An samu asarar rayukan ƴan gudun hijira mutum shida bayan wani ginin da su ke aune a ciki ya rufto musu. Ginin dai ya rufto ne bayan an yi ruwan sama mai yawa.
Wani mummunan rikici da ya barke a jihar Niger, ya janyo mutane da dama sun raunata, ya yin da dukiyoyi suka salwanta. Fadan ya barke ne tsakanin wasu bangarori
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum,ya garzaya garin Monguno tun ranar Alhamis inda ya duba yadda ake raba N275m, kayan abinci da sutturu ga IDPs.
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya gina wa jama'ar Malari gidaje 803 a kauyensu. Ya gwangwaje jama'ar N58.5m da kayan abinci ga magidanta.
Wata gagarumar gobara ta tashi a sansanin 'yan gudun hijira da ke Gamboru Ngala a jihar Borno, lamarin da yasa daruruwan 'yan gudun hijiran suka rasa matsuguni.
Gwamna Zulum ya yi wa masu 'yan gudun hijira a yankin Munguno ruwan kudi da kayan abinci. Gwamna ya zabi raba kudi ga mutanen da suka rasa harkoki kasuwancinsu.
Gwamnan jihar Borno tare da rakiyar wasu wakilai daga Najeriya sun isa kasar Kamaru domin dawo da 'yan gudun hijira 9,800 gida Najeriya. Sun isa ranar Talata.
Gwamnatin shugaba Buhari tana kokarinta wajen dawowa da 'yan gudun hijiran jihar Borno dake zaune a kasar Kamaru. An bayyana shirin dawo da sama da su 4,000.