Gwamnatin Buhari za ta dawo da 'yan gudun hijirar Borno 4,982 daga Kamaru

Gwamnatin Buhari za ta dawo da 'yan gudun hijirar Borno 4,982 daga Kamaru

- Gwamnain shugaba Buhari ta kudurta dawo da 'yan gudun hijara dake zaune a kasar Kamaru

- Gwamnatin ta bayyana cewa akalla 'yan gudun hijara 4,982 ne za ta dawo dasu gidajensu

- Gwamnatin tarayya na ci gaba da shirye-shirye da hukumomin kasar ta Kamaru don dawo da 'yan gudun hijira

Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Kasa (NCFRMI) ta fara aikin dawo da 'yan gudun hijirar Jihar Borno 4,982 da ke Kamaru, Daily Trust ta ruwaito.

Wata sanarwa a ranar Lahadi ta hannun mai ba da shawara na musamman kan harkokin yada labarai na NCFRMI, Sadiq Abdullateef, ta ce 3,224 daga cikin ‘yan gudun hijirar za su koma garin Banki; 1,758 kuma zuwa Bama, duk a cikin jihar Borno.

KU KARANTA: 'Yan sandan Kaduna sun kame masu satar motoci, an kwato wasu motoci

Gwamnatin Buhari za ta dawo da 'yan gudun hijirar Borno 4,982 daga Kamaru
Gwamnatin Buhari za ta dawo da 'yan gudun hijirar Borno 4,982 daga Kamaru Hoto: DW News
Asali: UGC

Ya ce wannan ya biyo bayan umarnin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar na cewa a gaggauta dawo da dukkan ‘yan gudun hijirar Najeriya da ke Kamaru zuwa gida cikin rayuwar mutunci da alfahari.

Ya ce Kwamishinan Tarayya na NCFRMI, Sanata Basheer Garba, a karshen mako ya gana da jami’an Kamaru da Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya a Maroua.

"Taron, wanda ci gaba ne na tarurruka a shekarar 2017 wanda kwamishina na lokacin ya fara a yanzu kuma Ministar Harkokin Jin Kai da Ci Gaban Jama'a, Sadiya Umar-Farouk, ya kuma kai ga nasarar dawo da 'yan Nijeriya 134 daga Kamaru."

Garba, wanda har ila yau shi ne shugaban kungiyar kwararru (TWG) ta Najeriya kan mayar da ‘yan gudun hijirar Najeriya, ya ce taron ya kasance mai share fage ne ga taron Kwamitin mai kusurwa uku (TC) da aka tsara gudanarwa a wannan makon.

KU KARANTA: Jama'ar gari sun cinna wa wani dan fashi da makami wuta a Yola

A wani labarin, Akalla likitocin mata 47 'yan jihar Kano sun dawo daga Sudan bayan sun kammala karatunsu cikin nasara wanda gwamnatin jihar ta dauki nauyi, Premium Times ta ruwaito.

Abba Anwar, babban sakataren labarai na gwamnan, ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa a ranar Asabar a Kano.

Sabbin daliban da suka kammala karatun aikin likita sun tafi kasar Sudan tun a shekara ta 2014 amma sun gamu da kalubale kan biyan kudade kafin gwamnatin Gwamna Abdullahi Ganduje ta warware dukkan matsalolin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel