Borno: Mummunar gobara ta kone sansanin 'yan gudun hijira, daruruwa sun rasa matsuguni

Borno: Mummunar gobara ta kone sansanin 'yan gudun hijira, daruruwa sun rasa matsuguni

  • Mummunar gobara ta tashi a sansanin 'yan gudun hijira da ke Gamboru Ngala a jihar Borno a ranar Lahadi da ta gabata
  • Gobarar ta lashe matsugunin daruruwan mutane kuma wasu sun samu raunika yayin kashe gobarar duk da ba a rasa rai ba
  • Hukumar SEMA ta jihar ta yi kira ga gwamnatocin tarayya da na jihar da su kai wa 'yan gudun hijiran tallafin gaggawa

Borno - Wata gagarumar gobara ta tashi a sansanin 'yan gudun hijira da ke Gamboru Ngala a jihar Borno, lamarin da yasa daruruwan 'yan gudun hijiran suka rasa matsuguni.

Daily Trust ta ruwaito cewa, lamarin ya auku da yammacin Lahadi inda gobarar ta lamushe wurare masu tarin yawa a sansanin.

Borno: Mummunar gobara ta kone sansanin 'yan gudun hijira, daruruwa sun rasa matsuguni
Borno: Mummunar gobara ta kone sansanin 'yan gudun hijira, daruruwa sun rasa matsuguni. Hotoo daga dailytrust.com
Asali: UGC

Wani jami'in hukumar taimakon gaggawa ta jihar, SEMA, da ke Gamboru Ngala, Malam Yusuf Gulumba, ya sanar da Daily Trust cewa an fara binciken abinda ya kawo gobarar.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ana fargabar tankar mai ta kashe wasu mutane da dama a wani hadari

Ya ce mutanen da suka samu kananan raunika ba su da yawa, sun kuwa jigata ne yayin da suke kokarin kashe wutar duk da ba a rasa rai ko daya ba.

Gulumba ya yi kira ga gwamnatocin tarayya da na jihar da su samar da kayayyakin abinci da na bukata tare da matsuguni ga wadanda ibtila'in ya fada wa.

Sansanin 'yan gudun hijira da ke Gamborun Ngala ya na da mutane sama da dubu arba'in kuma sun taba fuskantar gobara a watan Afirilun 2019.

Gobara ta kashe mutum 14 a sansanin 'yan gudun hijira a Borno

A wani labari na daban, 'yan gudun hijira 14 ne aka tabbatar da mutuwarsu yayin da 15 daga ciki suka samu raunika daban-daban. Hakan ya faru ne sakamakon barkewar gobara a sansanin 'yan gudun hijarar da ke karamar hukumar Ngala ta jihar Borno.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 15 a wani hari da suka kai jihar Neja

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta bayyana, gobarar ta fara ne da karfe 2:15 na yammacin ranar Alhamis a sansanin. Kamar yadda wata majiya ta tabbatar, an yi kokari wajen kashe wutar da gaggawa.

"A halin yanzu, ranar 16 ga watan Afirilun 2020, gobara ta kama a sansanin 'yan dudun hijira da ke Ngala. Gobarar ta lashe gidaje 1250 amma ba a tabbatar ba," majiyar ta ce.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng