Zulum da wasu sun isa Kamaru, don dawo da 'yan gudun hijirar Najeriya 9,800

Zulum da wasu sun isa Kamaru, don dawo da 'yan gudun hijirar Najeriya 9,800

- Gwamnan jihar Borno ya jagoranci tafiyar dawo da 'yan gudun hijra daga kasar Kamaru

- Gwamnan tare da wasu wakilai sun isa kasar Kamaru a ranar Talata 9 ga watan Fabrairu

- Gwamnan tuni ya ginawa 'yan gudun hijirar gidajen da zasu zauna a Banki da kuma Bama

Wakilan Najeriya sun isa Marwa, a Kamaru domin dawo da ‘yan gudun hijirar Najeriya 9,800, jaridar Punch ta ruwaito.

'Yan gudun hijra 9,800 sune wadanda ke cikin matakin farko na dawo da su daga Kamaru daga cikin ‘yan Najeriya 46,000 da ke samun mafaka a sansanin Minawao da ke kasar Afirka ta Tsakiya.

Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Borno, Malam Isa Gusau, ya fitar a ranar Laraba, ta ce maigidan nasa ya isa Marwa ne tare da jami’an ma’aikatar kula da ayyukan jin kai ta tarayya,da ci gaban jama’a don dawo da ‘yan Nijeriya 9,800 kasarsu.

Ya ce mutanen 9,800 sun kasance rukunin farko na ‘yan kasa da suka nuna aniyar a kwashe su don sake dawo dasu matsugunar da Gwamnatin Jihar Borno ta gina a garuruwan Bama da Banki.

KU KARANTA: Scholarship: Likitoci mata 47 'yan jihar Kano sun dawo bayan kammala karatu a Sudan

Zulum da wasu sun isa Kamaru, don dawo da 'yan gudun hijirar Najeriya 9,800
Zulum da wasu sun isa Kamaru, don dawo da 'yan gudun hijirar Najeriya 9,800 Hoto: PM News
Asali: UGC

Ya bayyana cewa Zulum ya isa Kamaru ne da yammacin Talata kuma a ranar Laraba ya jagoranci wakilan Najeriya zuwa wani taro kan wata yarjejeniyar da aka yi tsakanin Najeriya, Kamaru da Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya.

Yarjejeniyar wanda za a yi a Marwa a can arewa mai nisa Kamaru, tare da Gwamnan yankin arewacin Kamaru, Mijinyawa Bakare a matsayin mai masaukin baki.

Ya ce kafin tafiyarsa zuwa Kamaru, Zulum ya yi jerin ganawa da wasu Ministocin da abin ya shafa a Najeriya.

Mafi yawan 'yan gudun hijirar da ke sansanin Minawao galibi 'yan asalin jihar Borno ne kuma a koda yaushe suna rokon Gwamna Babagana Zulum da ya jagoranci dawo da su gida.

A watan Satumbar 2019, Zulum a yayin tafiyarsa zuwa sansanin ya yi wa 'yan gudun hijirar alkawarin zai amsa kiran rokon da suke yi tare da jawo hankalin masu ruwa da tsaki game da nasarar mayar da su da sake tsugunar da su cikin mutunci.

KU KARANTA: Wata sabuwa: Mabarata a jihar Jigawa sun hana gwamna fita daga cikin gidansa

A wani labarin, Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Kasa (NCFRMI) ta fara aikin dawo da 'yan gudun hijirar Jihar Borno 4,982 da ke Kamaru, Daily Trust ta ruwaito.

Wata sanarwa a ranar Lahadi ta hannun mai ba da shawara na musamman kan harkokin yada labarai na NCFRMI, Sadiq Abdullateef, ta ce 3,224 daga cikin ‘yan gudun hijirar za su koma garin Banki; 1,758 kuma zuwa Bama, duk a cikin jihar Borno.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel