Zulum ya yiwa 'yan gudun hijira a Munguno goma na arzika

Zulum ya yiwa 'yan gudun hijira a Munguno goma na arzika

- Gwamnan jihar Borno ya fidda makudan kudade ya kashe su duk akan wasu talakawan jiharsa

- Gwamnatin jihar ta ce ta rabawa magidanta da rikicin Boko Haram kudi kayayyakin abinci a Munguno

- An ce ya yi rabon kayan abinci da kudin ne duba da yadda mutanen yankin suka rasa harkokinsu

Gwamnan jihar ya ziyarci sansanonin gudun hijira dake yankin Munguno don tallafawa magidanta da kudade da kayan abinci.

Gwamnan, ya yi wa 'yan gudun hijira goma na arziki, inda ya raba zunzurutun kudi har N325m da kayyakin abinci ga talakawa magidanta sama da 100,000 wadanda 'yan ta'addan Boko Haram suka raba da matsugunansu.

Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Isa Gusau, ya fitar ya ce Gwamna Zulum ya dauki wannan matakin ne saboda tallafawa magidanta da suka rasa gonaki, gidaje da harkokin kasuwancinsu da sauran ababen rayuwa saboda rikicin Boko Haram.

KU KARANTA: Da dumi-dumi: Gwamna ya Ganduje ya raka Bola Tinubu zuwa fadar Sarkin Kano

Zulum ya yiwa 'yan gudun hijira a Munguno goma na arzika
Zulum ya yiwa 'yan gudun hijira a Munguno goma na arzika Hoto: bbc.com/hausa
Asali: UGC

An raba kudade da kayan abincin ne ga mutanen da suke zaune a sansanonin 'yan gudun hijira da ke Monguno, wadanda suka fito daga kananan hukumomin Kukawa, Marte, Ngnazi da Guzamala duk a jihar ta Borno, a cewar sanarwar.

Ya kara da cewa an raba dubban buhunan kayan abinci da sikari da zannuwa ga magidanta maza 65,000 da kuma mata 35,000, BBC Hausa ta rahoto.

Ba wannan bane karo na farko da Gwamna Zulum ke zuwa sansanonin 'yan gudun hijira domin ziyara da kuma yi musu alheri ba.

A baya Legit.ng Hausa ta ruwaito cewa, gwamna Zulum ya dira sansanonin 'yan gudun hijira tsakar dare domin tantance na gaskiya da na bogi.

KU KARANTA: Ta ya zai yiwu: Shenu Sani ya caccaki batun Tinubu na daukar sojoji miliyan 50

A wani labarin, An gano gwamna jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum a baya bayan nan ya tsaya tare da ayarin motocinsa ya taimakawa wasu mata da 'yan mata da ke diban itace a gefen titi.

A wasu hotuna da suka bazu a dandalin sada zumunta, an gano gwamnan kewaye da hadimansa suna taimakawa wasu mata.

Babu tabbas game da ranar da abin ya faru ko kuma wurin da ya faru amma hotunan sun dauki hankulan mutane da dama a dandalin sada zumunta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.