Jihar Imo
Kotun ƙoli ta ɗage sauraron ƙarar da jam'iyyar APGA ta shigar domin neman a tsige gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, na jam'iyyar APC mai mulki a jihar.
Wata jami’ar yar sanda ta yi fice a soshiyal midiya bayan ta rera taken kasa cike da kura-kurai a wani taron manyan jami’an yan sanda a jihar Imo.
Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a birnin Enugu, ta bayar da umarnin a maye gurbin Samuel Anyanwu a matsayin sakataren jam'iyyar PDP na ƙasa.
Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma ya mika kyautar asibiti sukutum ga coci don samun kulawa na musamman da kuma tausaya wa marasa lafiya da kula da shi.
'Yan bindiga sun hallaka mataimakin magatakardar Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke jihar Ebonyi, an kashe Innocent Obi ne a gidansa da ke jihar Imo.
Kwamitin gudanarwa na jam'iyyar PDP na ƙasa (NWC) ta musanta cewa ta kori sakataren jam'iyya na ƙasa, Sanata Samuel Anyanwu, ɗan takarar gwamna a Imo.
Mataimakin shugaban ƙasar Najeriya, Sanata Ƙashim Shettima da wasu gwamnonin jam'iyyar APC 14 sun sauka a jihar Imo yayin da APC zata kaddamar da kamfe.
Gabanin zaɓen 11 ga watan Nuwamba, 2023 a jihohin Imo, Kogi da Bayelsa, hukumar zaɓe INEC ta ce tabarbarewar tsaro da rikicin siyasa ya shige mata hanci.
Wasu miyagun ƴan bindiga sun cinnawa gidan wani babban ɗan majalisae wakilai wuta a jihar Imo. Ƴan bindigan sun sha alwashin cigaba da ta'addancinsu.
Jihar Imo
Samu kari