APC, PDP, LP: An Yi Hasashen Makomar Gwamna Uzodinma a Zaben Ranar Asabar

APC, PDP, LP: An Yi Hasashen Makomar Gwamna Uzodinma a Zaben Ranar Asabar

  • Hasashen wani mai fashin baki kan al'amuran siyasa ya nuna cewa gwamnan jihar Imo na yanzu, Hope Uzodinma ne zai sake lashe zaben gwamnan jihar karo na biyu
  • A cewar mai fashin bakin, ma damar ana batu kan zaben jihar Imo, to babu wanda zai iya dakatar da Uzodinma daga lashe zabe
  • Sai dai jam'iyyar adawa ta PDP ta ce tana da yakinin Uzodinma ba zai kai labari ba, la'akari da kowa ya juya masa baya, don haka dan takararta ne zai yi nasara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

An yi hasashen cewa Gwamna Hope Uzodinma shi ne zai lashe zaben gwamnan jihar Imo da za a gudanar ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Zaben 11 Ga Nuwamba: Jerin Gwamnonin Jihar Kogi Daga 1999 Zuwa Yanzu

Chizorom Ofoegbu, wani mai fashin baki kan al'amuran siyasa da aka fi sani da 'Ijele Speaks', yayi wannan hasashen yayin da ya ke tsokaci kan zaben jihar mai zuwa.

Zaben Jihar Imo
Mai fashin baki kan lamuran siyasa ya ce Hope Uzodinma ne zai lashe zaben jihar Imo karo na biyu Hoto: Hope Uzordinma, Samuel Anyanwu, Athan Achonu
Asali: Twitter

A zantawarsa da jaridar Legit, mai fashin bakin ya nuna yakininsa na nasarar Uzodinma a zaben.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Uzodinma ne zai yi nasara - Ofoegbu

Hasashen Chizorom Ofoegbu, na zuwa ne kasa da kwanaki hudu kafin zabukan gwamnoni da za a gudanar a wasu jihohin kasar, inda gwamnan jihar na yanzu ke kokarin ganin ya koma kan mulkin jihar karo na biyu.

Sai dai gwamnan na fuskantar manyan abokan karawa guda biyu a zaben jihar da za a gudanar ranar Asabar.

Ofoegbu ya ce:

"Ma damar ana batu kan zaben jihar Imo ne, to babu wanda zai iya dakatar da gwamna mai ci a jihar."

Kara karanta wannan

Rikicin Rivers: Fubara ya gana da Wike, Ya ce ‘mai gida na har gobe’

Mai Shari'a Dattijo ya kalubalancin nasarar Uzodinma a 2019

Sai dai, dan takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), , Samuel Anyawu da takwaransa na jam'iyyar Labour Party, Athan Achonu, sun nuna yakinin su na iya samun nasara a zaben da za a gwabza.

Idan ba a manta ba, dan takarar All Progressives Congress (APC), ya sha kaye hannun Emeka Ihedioha na jam'iyyar PDP a zaben 2019, inda ya kare a na hudu; sai dai kotu ta ba shi nasara, tare da ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar.

Wannan dalilin ya sa, Mai Shari'a Musa Dattijo Muhammad (mai ritaya) na kotun koli, wanda ya nuna kura kuran da ke cikin fannin shari'a na kasar, ya ce akwai bukatar yin nazari kan shari'ar gwamnan kogi da har kotin koli ta ba Uzodinma nasara.

PDP ta ce Uzodinma bai shahara a Imo ba

Kara karanta wannan

Kano: Kotun musulunci ta umurci magidanci ya karbi ɗan da ya ke kokwanton ba nasa bane

Jam'iyyar PDP, a nata bangaren, ta nuna cewar dan takararta ne zai yi nasara a zaben jihar Imo, inda ta kara da cewa al'umma sun juya baya ga gwamna mai ci da jam'iyyar APC.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa jam'iyyar adawar ta nuna cewa dukkan wasu alkaluma sun ayyana gwamnan a matsayin wanda zai sha kaye, wanda ya sa jam'iyyarsa ta fara tayar da rikici a jihar.

Na cika alkawuran da na dauka a Imo - Uzodinma

A wani bangaren kuma, Gwamna zodimma ya jaddada kudirin gwamnatinsa na ci gaba da inganta hukumar kula da ma’aikata ta jihar Imo da kuma sadaukarwa ga walwalar ma’aikata, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.

Da yake tsokaci kan kyakkyawan shugabanci, Gwamnan ya bayyana wasu daga cikin nasarorin da gwamnatinsa ta samu a bangaren ma'aikatan gwamnati.

Asali: Legit.ng

Online view pixel