IGP Ya Saka Dokar Takaita Zirga-Zirga a Jihohin Imo, Kogi, Bayelsa, an Jibge Jiragen Yaki Na Ruwa
- Sifeta Janar na rundunar 'yan sanda ya sanar da sanya dokar takaita zirga zirgar ababen hawa a johohin da za a gudanar da zabukan gwamnoni na ranar asabar mai zuwa
- Johohin da suka hada da Imo, Kogi da Bayelsa, shugaban 'yan sandan ya ce dokar za ta fara aiki daga ranar Juma'a mai zuwa har zuwa lokacin da za a kammala zaben
- Kazalika, ya ce hukumar ta tura jiragen yaki na ruwa da jiragen sama domin tabbatar da tsaro, don ganin an gudanar da sahihin zabe cikin lumana
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Sifeta Janar na rundunar 'yan sanda, Kayode Egbetokun, a ranar talata ya sanar da saka dokar takaita zirga-zirgar ababen hawa da jiragen ruwa, kwale-kwale da rufe sauran hanyoyin zirga-zirga a jihohin Imo, Kogi da Bayelsa, daga ranar Juma'a mai zuwa.
Egebtokun, wanda ya bayyana hakan, ya ce dokar na daga cikin matakan da za su dauka don ganin an gudanar da sahihin zabe kuma cikin lumana a jihohin uku.
Haka zalika, ya haramta wa wasu jami'an tsaron jihohi da suka hada da Ebubeagu da sauransu akan kaurace wa fita yin aiki a ranakun da ake gudanar da zaben.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sifetan, wanda ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a shelkwatar rundunar, ya bayyana cewa an tanadi jiragen yaki na ruwa a jihohin uku, don tabbatar da cewa ba a samu matsala daga bangaren tekuna ba.
Da ya ke jawabi ta bakin kakakin hukumar 'yan sanda, Olumuyiwa Adejobi, shugaban 'yan sandan, ya kuma tabbatar da cewa an kammala shiri na yin amfani da jiragen sama domin tabbatar da tsaro.
Shugaba Tinubu ya mika tutocin APC ga Ododo, Uzodinma da Sylva
Legit Hausa ta ruwaito maku yadda shugaban kasa Bola Tinubu ya mika tutocin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ga yan takarar gwamna uku na jam’iyyar gabanin zabukan da za a yi a wannan watan a jihohin Kogi, Imo, da Bayelsa.
Wadanda aka baiwa tutocin dai sune Gwamna Hope Uzodinma na Imo, wanda ya tsaya takara karo na biyu, Timipre Sylva na jihar Bayelsa da Usman Ododo na jihar Kogi, jaridar The Nation ta ruwaito.
Taron wanda ya gudana a cikin ɗakin taro na Banquet Hall na fadar shugaban ƙasa, ya samu halartar shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje, da sauran mambobin kwamitin gudanarwa na ƙasa na jam’iyyar (NWC), da wasu baƙin ƴan takarar.
Asali: Legit.ng