Abdulaziz Yari Ya Tona wa Gwamnatin Tinubu Asiri game da Sha’anin Rashin Tsaro
- Jam’iyyar ADC ta ce kalaman Sanata Abdul’aziz Yari kan matsalar tsaro sun nuna gazawar gwamnatin tarayya
- Daraktan yaƙin neman zaɓen APC, ya ce idan tsohon Muhammadu Buhari ya gaza, da wuya Bola Tinubu ya dace
- Kola Ologbondiyan yana ganin kalaman Yari sun nuna da wuya gwamnati ta iya magance matsalar rashin tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Majalisar yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa ta jam’iyyar ADC ta caccaki Gwamnatin Najeriya saboda batun tsaro.
ADC ta yi zargin cewa kalaman Sanata Abdulaziz Yari sun nuna gazawar mahukunta wajen kawo zaman lafiya a kasar nan.

Source: Getty Images
Maganganun Abdulaziz Yari sun tsokano ADC
Jam’iyyar ta ce Daraktan kamfen shugaban ƙasar ya nuna babu ingantattun hanyoyin magance rashin tsaro a cewar Daily Trust.
Kola Ologbondiyan ya bayyana hakan yayin da yake mayar da martani kan kalaman Yari game da tsaro da ya kai ziyara jihar Kebbi.

Kara karanta wannan
Gaskiya ta fito: Dalilin da ya sa 'yan majalisa 8 suka je wurin Tinubu bayan sun fice daga APC
Mista Ologbondiyan ya bayyana kalaman a matsayin babban suka ga gwamnatin APC mai-ci.
Ya ce kalaman Yari sun haifar da tambayoyi masu muhimmanci game da karfin APC na magance rashin tsaro da ake kuka da shi.
Jam'iyyar ADC tana adawa da zarcewar APC
Darektan na kamfe ya nemi jin dalilin da ya sa take neman sake samun sabon wa’adin mulki zuwa shekarar 2031 a zabe mai zuwa.
Ya ce bai kamata jama’a su sake ba wa gwamnatin da ta gaza samar da isasshen tsaro da sauƙaƙa matsin tattalin arziki wani wa’adi ba.
Ya ce:
“Ga jam’iyyar da ta shafe kusan shekaru 12 tana mulki, wannan furuci ne mai ban mamaki da ke nuna amincewa da gazawa.
"Maimakon ya ƙarfafa wa ’yan Najeriya gwiwa, furucin daraktan yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC ya ƙara ƙarfafa ra’ayin cewa jam’iyyar mai mulki ta rasa dabarun magance matsalolin tsaron ƙasar."
Daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na ADC-PCC ya jero matsalolin da ake fama da su ba a shawo kansu da duk da alƙawura.

Kara karanta wannan
Sanata ya tabbatar da abin da ake tsoro a APC, ya ce akwai matsaloli cikin jam’iyyarsu
“Bayan shekaru ana yin alƙawura, har yanzu ’yan Najeriya na fuskantar ’yan bindiga, ta’addanci, garkuwa da mutane da kashe-kashen da ake yi ba tare da nuna ƙauna ba.
Najeriya na buƙatar shugabancin da zai ɗauki alhakin matsalar tsaro, ya samar da mafita mai amfani, sannan ya nuna ƙudurin kare jama’a.
Punch ta rahoto shi ya ce al’ummomi na ci gaba da kasancewa cikin barazana, iyalai na rayuwa a tsorace baya ga matsin tattalin arziki.
Kakakin ya ƙara da cewa ƙasar ba ta buƙatar gwamnati ko jam’iyyar da za ta riƙa bayar da uzuri kan ci gaba da tabarbarewar tsaro.

Source: Getty Images
Fargabar da 'yan jam'iyyar APC suke da shi
Gabanin babban zabe mai zuwa na shekarar 2027, an ji labari cewa jam'iyyar APC na fuskantar matsaloli a cikinta fiye da na ’yan adawa.
Ali Muhammad Ndume ya tabbatar da fargabar da Kashim Shettima yake da shi a filin zabe saboda sharri da zagon-kasa daga cikin gida.
Wasu manyan APC sun fi tsoron zagon kasa daga ‘ya ‘ya a kan ‘yan adawa a takarar da ake ganin zai zama tsakaninta da ADC da NDC.
Asali: Legit.ng