Shugabannin Kananan Hukumomi 21 da Kansiloli fiye da 200 Sun Fice daga PDP zuwa APC
- Shugabannin ƙananan hukumomi 21 da kansiloli 226 a jihar Adamawa sun fice daga PDP zuwa APC mai mulki
- Ciyamomi da kansililin sun ce sun ɗauki matakin ne bayan tattaunawa da iyalansu da abokan siyasa
- Jam'iyyar APC ta ce sun sauya sheƙa ne domin su kasance a jam’iyya ɗaya da ubangidansu na siyasa, Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Adamawa, Najeriya - Duka shugabannin ƙananan hukumomi 21 da kansiloli 226 a jihar Adamawa sun yi murabus daga jam’iyyar PDP tare da komawa APC mai mulki.
Mafi yawan ciyamomin sun sanar da ficewarsu daga PDP a ranar Litinin ta hanyar wasiƙun murabus da suka aika wa shugabannin jam’iyyar na mazabunsu a ƙananan hukumomi 21 na jihar.

Source: Twitter
A wasu daga cikin wasiƙun murabus ɗin da wakilin Daily Trust ya gani, shugabannin sun bayyana cewa sun ɗauki matakin ne saboda dalilai na kansu bayan tattaunawa da iyalansu da abokan hulɗarsu ta siyasa.
Dalilin sauya shekar ciyamomi 21
A cikin wasiƙar murabus ɗinsa, shugaban Ƙaramar Hukumar Demsa, Akham Jalo, ya ce ya yanke shawarar barin PDP zuwa jam’iyyar APC ne bayan tattaunawa da iyalansa, abokan siyasa, masu ruwa da tsaki da kuma al’ummar Demsa.
Ya ce:
“Shawarar da na yanke ta komawa APC ta samo asali ne daga buƙatar haɗa kai da hangen nesan Mai Girma Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri, domin jawo ƙarin romon dimokuraɗiyya ga al’ummar Demsa.
“Wannan sauyin siyasa an yi shi ne domin ci gaban kowa da kowa, haɗin kai da bunƙasa al’umma, kuma gwamnatina za ta ci gaba da jajircewa wajen kyakkyawan shugabanci, zaman lafiya da walwalar jama’a,” in ji Jalo.
Jalo ya nuna matuƙar godiya ga shugabanni da mambobin PDP bisa damar da suka ba shi ta yi wa al’umma hidima.
Ya kuma tabbatar wa al’ummar Demsa cewa komawarsa APC zai buɗe sababbin ƙofofin damarmaki tare da hanzarta ci gaban ƙaramar hukumar.
APC ta tabbatar da sauya sheƙar
Da yake tabbatar da lamarin, Sakataren Yaɗa Labarai na APC a jihar Adamawa, Victor Dogo, ya ce dukkan shugabannin ƙananan hukumomi 21 sun koma jam’iyyar a ranar Litinin, 19 ga Oktoba 2026.

Source: Getty Images
Dogo ya danganta sauya sheƙar da matakin da suka ɗauka na “haɗa kai da ubangidansu na siyasa, Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri, wanda ya kasance tare da su a kowane lokaci.”
Ya ce:
“Dukkan shugabannin ƙananan hukumomi 21, masu kula da hukumomin ci gaban yankuna da kansiloli 226 na jihar Adamawa sun shigo jam’iyyar APC.
APC ta lashe zaben ciyamomi a Kogi
Kun ji cewa jam’iyyar APC ta lashe dukkan kujerun shugabannin ƙananan hukumomi 21 da kuma kujerun kansiloli 239 a jihar Kogi.
Shugaban hukumar zaɓen jihar, Mamman Eri, ya sanar da sakamakon a Lokoja, inda ya yaba wa jami’an tsaro, masu sa ido da sauran masu ruwa da tsaki
Asali: Legit.ng

