Babbar Magana: Netanyahu Ya Yi Sabuwar Barazana ga Jagoran Iran, Mojtaba Khamenei
- Benjamin Netanyahu ya yi barazana ga Mojtaba Khamenei, sabon jagoran addini na Jamhuriyar Musulunci ta Iran
- Ya zargi sabon jagoran Iran da bin sawun mahaifinsa, Ayatollah Ali Khamenei, wanda aka kashe a harin sama a farkon yaƙin Amurka da Isra’ila kan Iran
- Kalaman sun fito ne yayin da Netanyahu ke shirin tunkarar zaɓen Isra’ila, tare da ci gaba da fuskantar shari’ar zargin cin hanci da rashawa da yake musantawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Tel-Aviv, Israila - Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya yi barazana ga Jagoran Addinin Iran, Mojtaba Khamenei.
Benjamin Netanyahu ya yi barazana ga Mojtaba Khamenei ni a wani bikin yaye jami’an sojojin Isra’ila.

Source: Getty Images
Wani saƙo da aka wallafa a shafin X na ofishin Firaministan Israila a ranar Laraba, 21 ga watan Oktoban 2026 ya nuna hakan.
Barazanar Netanyahu ga Mojtaba Khamenei?
Da yake jawabi a wajen bikin, Benjamin Netanyahu ya ce gwamnatin Iran har yanzu ba ta koyi darasi daga abubuwan da suka faru ba.
Benjamin Netanyahu, wanda Kotun hukunta manyan laifuffukan yaki ta duniya (ICC) ke nema bisa zarge-zargen aikata laifukan yaƙi a Gaza, ya ce har yanzu gwamnatin Iran ba ta koyi darasi ba.
Netanyahu ya zargi Mojtaba Khamenei da zalunci
Netanyahu ya kira Mojtaba Khamenei da kalmar da ke nufin “azzalumin wannan zamani”, yana mai cewa sabon jagoran Iran ya zaɓi bin sawun mahaifinsa, tsohon Jagoran Addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei.
An kashe Ayatollah Ali Khamenei ne a wani harin sama a ranar farko ta yaƙin da Amurka da Isra’ila suka fara kan Iran a ƙarshen watan Fabrairun 2026.
Netanyahu ya ce Mojtaba Khamenei ya “cire makullin aminci”, wata magana da ya yi amfani da ita wajen bayyana abin da ya kira ƙara tsananta barazanar Iran.
Ya ƙara da cewa hanya ɗaya tilo ta kawar da wannan barazana ita ce hambarar da gwamnatin Iran.
Firayin Minista zai fafata a zaɓen Israila
Kalaman Netanyahu sun zo ne a daidai lokacin da yake ƙoƙarin tabbatar da makomarsa ta siyasa, yayin da yake neman sake samun nasara a zaɓen Isra’ila mai muhimmanci da ake shirin gudanarwa a mako mai zuwa.
Baya ga matsin siyasa, Netanyahu yana fuskantar shari’a kan wasu zarge-zargen cin hanci da rashawa, waɗanda ya musanta.
Kalaman nasa kan jamhuriyar Musulunci ta Iran na zuwa ne yayin da rikicin da ke tsakanin Isra’ila da Iran ke ci gaba da kasancewa babban batu a harkokin tsaro da siyasar Gabas ta Tsakiya.

Source: Twitter
Iran ta kama jirgin Amurka a Hormuz
A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar juyin juya halin Musulunci ta Iran ta ce ta kama wani jirgin ƙarƙashin ruwa mara matuƙi na Amurka a ƙofar Mashigar Hormuz.
An bayyana jirgin a matsayin Dive-LD, wani babban jirgin ƙarƙashin ruwa mai cin gashin kansa da kamfanin tsaro na Anduril da ke California ya ƙera.
Asali: Legit.ng

